Turkiya: Gyara ga kundin tsarin mulki
March 27, 2017In har sakamakon kuri'ar raba gardamar ya amince da yi wa kundin tsarin mulkin Turkiyan kwaskwarima, hakan zai ba wa Shugaba Recep Tayyip Erdogan damar fadada ikonsa. A nan Jamus 'yan kasar ta Turkiyya su kimanin sama da miliyan guda da suka cancanci kada kuri'a, za su sauke wannan nauyi a kananan ofisoshin jakadancin kasar da ke fadin Jamus. A can Turkiyya a ranar 16 ga watan Afrilu za a kada kuri'ar raba gardamar a kan kwaskware kundin tsarin mulkin. Wata takaddama a kan gangamin yakin neman zabe da 'yan siyasar Turkiyya a Jamus suka so yi, ta janyo tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu lamarin da ya sa Shugaba Erdogan ya soki Jamus da bin manufofin 'yan Nazi, kalaman kuma da 'yan siyasa a Jamus din da ma nahiyar Turai suka yi tir da su.