1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Turai ta yi fushi da China kan daure 'yar jarida

December 29, 2020

Kungiyar Tarayyar Turai ta EU ta bukaci hukumomin China da su yi gaggawar sakin 'yar jaridar da aka daure saboda bayar da labarin cutar corona, Zhang Zhan.

https://p.dw.com/p/3nL6n
China Journalistin Zhang Zhan
Hoto: YOUTUBE/AFP

Sanarwar ta EU din ta wannan Talata ta kuma bukaci China ta sako wasu karin 'yan jarida da lauyoyi da kuma 'yan fafutuka da kasar ke tsare da su. 


Mai magana da yawun bangaren huldar jakadanci na kungiyar ta EU Peter Stano ya ce kungiyar ta samu bayanin da ke cewa ana gasawa 'yar jarida Zhang aya a hannu a zaman da take yi a hannun hukumomi.


A ranar Litinin ne dai China ta zartawa da 'yar jaridar hukuncin daurin shekaru hudu saboda kawo labarai masu rudani a lokacin annobar corona a Wuhan.