1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Muna bukatar tabbaci a shari'ance

Zainab Mohammed Abubakar
February 18, 2019

A martaninsa ga kiran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi, ministan harkokin wajen Jamus ya ce, zai kasance abu mawuyaci Turai ta karbi 'yan asalin nahiyar da suka hade a kungiyar IS a Siriya

https://p.dw.com/p/3DapT
Rumänien EU - Aussenministertreffen
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Alexandru

Heiko Maas ya ce hakan zai auku ne kawai, idan har sun samu tabbacin cewar, za'a tsare tare da gurfanar da irin wadannan mutanen a gaban kotu da zarar an turosu.

Ya ce wajibi ne su samu bayanai a shari'ance, kuma a yanzu ba haka lamarin yake ba. Gwamnatin Berlin na neman tuntubar Faransa da Birtaniya, domin sanin alkiblar da za'a dosa kan wannan batu.

Za'a gabatar da wannan batu kazalika a taron ministocin harkokin waje na Kungiyar Tarayyar Turan da ke gudana a wannan Litinin, domin nazarin wasu batutuwa ciki har da halin da ake ciki a Siriya.

A wannan Lahadin ce dai shugaba Trump ya yi kira ga Turai da ta karbi 'yan asalin kasashenta da ake zargi sun hade a kungiyar IS.