Tura ta kai bango a Siriya
July 27, 2012Rahotannin daga Siriya na cewar dakarun gwamnatin Bashar Al Assad sun sake kai wani farmaki na ruwan bama bamai ta jiragen sama masu saukar ungula da jijifi a birnin Alepo birnin na biyu mafi girama´na ƙasar.
Wani ɗan adawar ya shaida wa kamfanin dilancin labarai na Faransa AFP cewar ya ga tankokin yaƙi kusan guda ɗari da suka shigo birnin na Alepo. Amurka ta baiyana fargabanta akan yiwar aikata kisan kiyasu na sojjin gwamnatin akan farar hula a unguwanin birnin da galibi yan tawaye suka yi shelar iko da su. masu aiko da rahotanin sun ce jama'a maza da mata da yara na ta tsrewa daga yanki a cikin manyan motoci gabannin bata kashin; ta ɗaukar ma rai ,da ake shirin yin tsakanin sasan biyu masu gaba da juna.
A halin da ake ciki kuma wasu rahotanin na cewar wata yar majalisar dokokin daga garin Alepo,Ilkas Al Badaoui ta canza sheƙa domin bin bayan sahun yan adawa kuma ma har ta tsallaka zuwa ƙasar Turkiya.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu