Tunisiya ta hana jiragen Libiya shiga kasarta
March 24, 2015Tunisiya ta sake rufe hanyoyin sufurinta na sama da Libiya, kwanaki kadan bayan da ta amince jiragen Libiyan da suka shafe watanni shidda a kasar su koma Tripoli. Wannan matakin ya zo ne sakamakon harin da aka kai gidan tarihin Tunis, wanda ya kai ga hallakar 'yan yawon bude ido 20. Majiyoyin tsaro sun bayyanawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa biyu daga cikin 'yan bindigan sun sami horo ne a wani sansanin horaswar IS da ke Libiya.
Tunisiya na fargabar kada tashe-tashen hankulan da suka addabi Libiya su shafeta musamman ganin yadda har yanzu, bangarori biyu ke kokuwar rike madafun ikon kasar ko bayan shekaru hudu da mutuwar Mu'ammar Gaddafi.
Wannan mataki zai kuntatawa 'yan Libiya da dama wadanda sukan tsere zuwa Tunisiya domin kauracewa matsalar tsaron kasarsu