1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTunusiya

Tunisiya ta dage ziyarar tawagar EU kan bakin haure

September 30, 2023

Shugaban kasar Tunisiya Kais Said ya yanke shawarar dage ziyarar da tawagar EU ta shiya kai wa kasar domin nazari kan yarjejeniyar da bangarorin biyu suka kulla kan dakile kwararar bakin haure.

https://p.dw.com/p/4X0iV
Tunisiya ta dage ziyarar tawagar EU kan dakile kwararar bakin haureHoto: Van den Bergh/ANP/picture alliance

A cikin wata sanarwa an ambato wani ministan kasar na cewa har yanzu da akwai rashin jutuwa tsakanin Tunisiya da hukumar Tarayyar Turai kan wasu muhunmnan batutuwa da ke kunshe a cikin yarjejeniyar da aka cimma a watan Yulin da ya gabata.

Karin bayani: Yarjejeniyar EU da Tunisiya kan 'yan gudun hijira

Daga nata bangare hukumar EU ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da hukumomin na Tunisiya don sake tsayar da lokacin da ya dace don aike wa da tawaga domin kammala yarjejeniyar.

A karkashin yarjejeniyar dai EU ta yi alkawarin ba wa Tunisiya tallafi na kudin da ya kai miliyan 105 na Yuru domin tada komadar tattalin arzikinta, kuma ko da a tsakkiyar wannan mako hukumar ta sanar da ware wasu miliyan 42 na Yuru da za ta bai wa Tunusiyar cikin gaggawa.