1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin rashin tabbas a Mali bayan boren 'yan adawa

Gazali Abdou Tasawa MNA/FD
July 13, 2020

Jagoran masu zanga-zangar kyamar gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita a Mali wato Imam Mahmoud Dicko ya yi kira ga 'yan kasar da su kwantar da hankalinsu su kuma kauce wa lalata kadarorin gwamnati a lokacin zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/3fFTf
Mali Bamako Proteste gegen die Regierung
Hoto: Getty Images/AFP/M. Cattani

Mutane 11 ne dai hukumomin babban gidan asibitin birnin Bamako suka tabbatar sun mutu wasu 124 suka ji rauni a tsawon kwanaki uku na zanga-zangar kyamar gwamnatin ta Ibrahim Boubakar Keita wacce ta rikide zuwa tarzoma. Daruruwan jama'a dai ne kuma suka halarci jana'izar wasu daga cikin wadanda suka mutun a lokacin tarzomar. Sai dai kuma bayan jana'izar jagoran masu zanga-zangar Imam Mahmoud Dicko ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankali su kuma nuna dattaku a gwagwarmayar da suke.

"Ina kira ga matasan kasar Mali da al'umma kasar baki daya da su nuna dattaku domin kamar yadda na fada masu tun a lokacin zanga-zangarmu ta ranar 19 ga watan Yuni, muna iya nuna karfinmu ba tare da mun aikata barna ba. Dan haka nake rokonsu da su dakatar da kone-kone da farfashe-farfashen da suke yi."

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita
Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar KeitaHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Kawo yanzu dai kura ta dan lafa a birnin na Bamako. Kuma kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da Kungiyar Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai sun bayyana damuwarsu da halin da ake ciki a birnin na Bamako tare da yin Allah wadai da yadda bangarorin da ke hamayya da juna ke amfani da karfi kan junansu. Kazalika sun yi kira da a sako shugabannin 'yan adawar kasar da aka kama. Daga nashi bangare jagoran masu zanga-zangar Imam Mahmoud Dicko ya ce ba za su ki sauraran kiraye-kirayen da ake yi masu ba amma kuma kokowar da suke ba ja da baya.

"Ba za mu manta da kiraye-kirayen da kasashe aminan Mali ke yi mana ba, da wadanda ke aiko mana sako na ganin mun nuna dattaku cikin wannan lamari. Lallai mun san wannan shawara ce ta gari kuma za mu yi kokarin kiyaye wa. Amma dai  kokowar da muke yi ba ja da baya. Muna yin ta ne domin maido da kimar kasar Mali, da kawo karshen wannan mulkin ta yadda durkushewar da kasar ta kama yi kar ta tabbata."

A kokarin da yake na yayyafa wa wutar rikicin ruwa, Shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya rusa kotun tsarin mulkin kasar da ke zama daya daga cikin bukatun masu zanga-zangar. Sai dai da bisa dukkan alamu wannan mataki kadai bai gamsar da magoyan bayan Imam Mahmoud Dickon ba kamar dai yadda Dramane Diarra ya nunar.

"Ya ki ya rabu da firaministansa, ya ki rusa majalisar dokoki, yanzu ta kai ga hallaka 'yan kasa. Mutane sun kona majalisar dokoki. Duk barnar da aka aikata yana da alhaki domin da dai ya saurari kukan jama'a da ba mu kawo inda muke ba yau. Amma Ibrahim Boubacar Keita ya san da cewa in bai ji bari ba to ya ji hoho."

Imam Mahmoud Dicko da magoya bayansa a lokacin zanga-zanga
Imam Mahmoud Dicko da magoya bayansa a lokacin zanga-zangaHoto: Reuters/M. Rosier

To sai dai a daidai lokacin da wasu 'yan Malin ke neman shugaban kasa ya yi murabus wasu na ganin da wuya a iya shawo kan matsalolin kasar a cikin wannan yanayi na tarzoma. Modibo Kadioke na daga cikin masu irin wannan ra'ayi.

"Matsalolin Mali masu sarkakkiya ne kuma masu yawa ne da ba za a iya shawo kansu a cikin kasa wacce kawunan jama'a ke rarrabe ba. Ya kamata shugaban kasa ya fahimci haka, kuma shekaru uku suka yi masa saura a wa'adin mulkin nasa, ya gaggauta daukar matakan hada kan 'yan kasar a cikin wadannan shekaru uku."

A yanzu dai ana sa ran lamurra za su ci gaba da lafawa bayan da kungiyoyin masu zanga-zangar suka bayyana amincewarsu da wasu shawarwari da tawagar jami'an Ecowas a kasar suka bayyana da suka hada da kafa gwamnatin hadin kan kasa da sake gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a garuruwan da kotun tsarin mulkin kasar ta soke zabensu na watannin Maris da Afrilu, batun da shi ne ya yi sanadiyyar barkewar zanga-zangar wacce ta rikide zuwa tarzoma a kasar ta Mali.