Tsohon zakaran duniya Anthony Joshua ya doke Francis Ngannou
March 9, 2024Tsohon zakaran damben duniya Anthony Joshua ya doke abokin karawarsa Francis Ngannou na Kamaru, a fafatawar da suka yi a Kingdom Arena da ke birnin Riyadh na kasar Saudi Arebiya a daren Juma'a.
Karin bayani:Wasanni: Damben boxing da wasan guje-guje da kwallon kafa
Bayan gwabzawar ne sai suka rungumi juna inda suka tattauna. Daga bisani Anthony Joshua ya shaidawa 'yan jarida cewa ya shawarci Francis Ngannou da ya ci gaba da damben domin akwai alamun nasara a nan gaba.
Karin bayani:Dambe: Mayweather ya doke McGregor
Wannan dai ita ce fafatawa ta biyu da Francis Ngannou ke yi a fagen damben, bayan barin wadda ya yi fice a cikinta wato MMA da ake amfani da hannu da kafa wajen duka.
A dambensa na farko dai sauran kiris ya samu nasarar doke zakaran duniya Tyson Furry bayan ya kai shi kasa.