1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon Shugaba Issoufou ya juya wa Bazoum baya

Salissou Boukari MAB
September 26, 2023

Matakin tsohon shugaban Nijar Mahamadou Issoufou na shirya gangamin nuna goyon baya ga sojojin da ke mulki na ci gaba da daukar hankali da martini inda wasu ke ganin cewa alama ce ta neman komawa gidan jiya a kasar.

https://p.dw.com/p/4WpPa
Hambararren Shugaba Mohamed Bazoum da tsohon Shugaba Mahamadou Issoufou
Hambararren Shugaba Mohamed Bazoum da tsohon Shugaba Mahamadou Issoufou Hoto: Aboubacar Magagi

Gishiri ya kama kan kaza dangane da yunkurin tsohon shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou da ya bijiro da shirin kawo goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulki. Dama tun a baya, jama'a na nuna shakkunsa kan lamarin, ganin cewa wadanda suka yi  juyin mulkin sun yi gadin fadar shugaban kasa na tsawon shekaru karkashin Issoufou da ma Bazoum. Amma wannan sabon kutse na tsohon shugaban kasa ya sanya wasuhadiman Bazoumna ganin cewar akwai lauje cikin nadi, ciki har da Sahanine Mahamadou wani na PNDS-Tarayya ta yi martani ga firaministan da hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum.

Karin bayanPNDS Tarayya ta yi martani ga firaministai: 

Jam'iyyar PNDS-Tarayya ta shiga wadi na tsaka mai wuya a Nijar
Jam'iyyar PNDS-Tarayya ta shiga wadi na tsaka mai wuya a NijarHoto: DW/D. Köpp

Sai dai na hannun daman tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou suka ce ba shi ne ya yi wannan kira ba, amma jam'iyyar PNDS-Tarayya ce ta yi kiran. Amma Zakari Oumarou tsohon gwamnan jihar Maradi kuma mashawarci a fadar shugaban kasar da aka hambarar ya ki cewa uffan  domin ba shi ne shugaban kwamitin ba. A nasu bangaren, 'yan kungiyoyin farar hula da ke fafutikar neman 'yancin kasar Nijar ta hanyar samun sabuwar akibla da sabon yanayi na tafiyar da mulki na ganin wannan lamari na jam'iyyar PNDS-Tarayya a matsayin batu da ba za a yarda da shi ba, a cewar Dambaji Son Allah.

Karin bayanNijar da Faransa an raba gari kwata-kwatai: 

Janar Abdourahmane Tiani ya yi maraba da shirin Faransa na janye sojojinta
Janar Abdourahmane Tiani ya yi maraba da shirin Faransa na janye sojojintaHoto: REUTERS

Wannan cece-kuce na zuwa ne daidai lokacin da kasar Faransa ta janye sojojinta daga Nijar da kuma jakadanta, lamarin da ya sa hukumomin na Nijar maida martani ta bakin Kanal Amadou Abdourahamane da ke magana da yawun sojojin na hukumar CNSP. A hannun daya kuma baraka na ci gaba da tabbata a jam'iyyar PNDS-Tarayya da ta mukii kasar ta Nijar sama da shekaru 12 da suka wuce, inda yanzu ta tabbata cewa ba a ga maciji tsakanin hambarren shugaban kasar Mohamed Bazoum da tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou.