Duniya na jimamin mutuwar Jimmy Carter
December 30, 2024Amurka na cikin alhinin mutuwar tsohon shugaban kasar Jimmy Carter wanda ya rasu a jiya Lahadi yana da shekaru 100 a duniya a mahaifarsa da ke Gojiya.
Jimmy Carter ya kasance shugaban Amurka na 39, kuma ya ja ragamar kasar daga shekarar 1977 zuwa 1981 bayan an zabe shi a 1976 inda ya yi wa'adi mulki guda daya.
A lokacin da yake raye ya yi futuka matuka gayya wajen shinfida zaman lafiya a sassa daban-daban na duniya ciki har da jagorantar yarjejeniyar sulhu tsakanin Isra'ila da Masar a watan Maris na 1979.
Bayan saukarsa daga kan garagar mulkin fadar White House Jimmy Carter ya kafa gidauniyarsa ta Carter don ingantuwar zaman lafiya da magance rikice-rikice a duniya lamarin da ya kai shi ga lashe kyautar zaman lafiya ta Prix Nobel a shekarar 2002.
Tun bayan sanar da rasuwar tsohon shugaban mafi shekaru a tsofin shugabannin Amurka, shugabannin kasashe da hukumomi na duniya na bayyana alhini tare da yaba masa bisa ayyukan alheri da ya yi a zamanin rayuwarsa.
Tuni ma Shugaba mai barin gado na Amurka Joe Biden ya ayyana ranar tara ga watan Janairu na 2025 a matsayin ranar makoki a fadin kasar domin girmama marigayi Jummy Cater.