1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Tsarin tsaftace Ka’abah da Harami

Mahmud Yaya Azare RGB
April 20, 2021

Saudiya ta gabatar da sabbin dabarun tsaftace Ka'aba da farfajiyar Harami a kokarinta na saukakawa maniyata da masu ziyara ayyukan ibada tare da karesu daga cututtuka.

https://p.dw.com/p/3sHaO

Mahukuntan Saudiya sun gabatar da sabbin dabarun tsaftace Ka'aba da farfajiyar Harami cikin karamin lokaci da kuma busar da shi, ba tare da an samu dogon tsaiko ga masu ibada ba, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Saudiya ya bayar da rahoton. A karon farko a tarihi an gudanar da aikin wanke dakin Ka’aba da farfajiyar masallacin harami mai tsarki a cikin lokaci mafi karanci, inda ma’aikatan da suke kula da tsaftar wurare masu tsarki su kimanin dubu hudu suka gudanar da aikin a cikin kasa da mintuna biyar suka kuma kamala.