Tsananin zafin da wasu kasashen Turai ciki har da Jamus ke fuskanta a halin yanzu ya janyo asarar miliyoyin euro ga manoma da kuma masu sufurin jiragen ruwa. Shuke-shuke na furanni da bishiyoyi a cikin gari da wuraren shakatawa duk sun fara bushewa. Mazauna a birnin Bonn sun yi tururwa zuwa wuraren da ke da dausayi. Ahmed Salisu ya hada mana rahoto kan wannan batu.