1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan majalisar Ghana na son yin aiki daga gida

Inshola Yussif Abdul Ganiyu ZUD/ZMA
November 8, 2022

'Yan majalisar dokokin Ghana sun bukaci a ba su damar yin aiki daga gida sakamakon tsadar man fetur da kasar ke fuskanta. Hakan na zuwa ne a yayin da jama'ar kasar ke nuna bacin ransu a kan matsalar.

https://p.dw.com/p/4JCUS
Ghana Präsident Nana Addo Dankwa Akufo-Addo
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-AddoHoto: Anthony Anex/KEYSTONE/picture alliance

Wasu 'yan majalisar dokokin Ghana na rokon shugabannin majalisar kasar su ba su izinin yin aiki daga gida sakamakon gazawar gwamnati ta mayar da farashin man fetur  yadda yake a baya. 'Yan majalisar sun bayyana haka ne ta bakin  wakilin mazaban Asuogyman da ke jihar gabas, Hon .Thomas Nyarko Ampem, wanda ya ce kwana biyu kadai ne ya kamata majilisa ta yi aiki idan aka yi la'akari da tsadar man fetur din da kasar ke fuskanta.  

Wannan matsala ta tsadar man dai ana ganin ta haifar da gagarumin koma-baya ga harkokin tattalin arzki na jama'a da ma gwamnati kuma da alama za ta ci gaba bunkasa har zuwa lokacin da za a shawo kanta in ji masana tattalin arziki .

Amina Adongo da ke zaune a birnin Kumasi ta shaida wa DW cewa idan har 'yan majalisa da jama'a ke wa kwallon suna cikin wadata za su nemi su yi aiki daga gida saboda tsadar fetur, to ya talaka zai yi da rayuwa ke nan? Ta ce ''ya kamata gwamnati ta duba batun domin matsalar na iya girma ta wuce sanin gwamnati.''

Wani mai fafutukar yaki da talauci a Ghana Alhaji Oga Suleimana ya ce idan har da gaske matsalar ta damu 'yan majalisar to sun san matakan da za su iya bi su tsige shugaban kasa idan har ya ci gaba da kawar da kai ga matsalar tsadar man fetur din da kasar ke fuskanta.