1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya sami beli bayan tsare shi a gidan yaki

August 25, 2023

An tsare Donald Trump na wani dan lokaci a birnin Atlanta bisa zarginsa da yunkurin sauya sakamakon zaben shekarar 2020 a Georgia

https://p.dw.com/p/4VYn7
Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump
Jami'an tsaron Amurka sun kai Danald Trump gidan kaso Hoto: Fulton County Sheriff's Office/Getty Images/AFP

Jami'an tsaro a Amurka sun tsare tshohon shugaban kasar Donald Trump na wani dan lokaci a birnin Atlanta, bisa zarginsa da yunkurin sauya sakamakon zaben shugaban kasar na shekarar 2020 a Georgia kafin daga bisani su sallame shi bayan biyan kudin beli.

Karin bayani:

Trump na fuskantar tuhuma a Georgia.

A lokacin da suka tsare shi, jami'an tsaron sun mika Donald Trump a wani gidan kaso na birnin Atlanta inda aka dauki hotonsa, abin da ke zama na farko ga wani tsohon shugaban kasa a tarihin Amurka. Kotu ta zartar da hukunci a kan Trump

Bayan belinsa bisa biyan dala 200.000, Trump ya gaggauta ficewa daga gidan kason tare da rakiyar ayarin motocin jami'an tsaro.

A lokacin da yake daukar jirgi domin barin birnin, Donald Trump ya yi tir da tuhumar da ake yi masa, yana mai zargin gwamanatin shugaba Joe Biden da goga masa kashin kaji don dakushe tasirinsa tare kuma da hana masa tsayawa takara a zaben 2024.