1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta ja nunnen Turkiyya kan Siriya

Abdul-raheem Hassan
October 10, 2019

Dakarun Turkiyya sun kashe mayakan Kurdawan Siriya 16 bayan kaddamar da hare-hare a yankunan da ke kan iyakar kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/3R0di
Militäroffensive der Türkei in Nordsyrien
Hoto: Getty Images/B. Kara

Ma'aikatar tsaron Turkiyya ta ce dakarunta sun killace wani ayarin Kurdawa sama da 200 da ta ke zargi 'yan ta'adda ne, an kuma girke manyan tankokin yaki a muhimman wurare.

Sai dai Shugaban Amirka Donald Trump ya ce Turkiyya ta yi kuka da kanta idan ba ta bi a sannu ba yayin kaddamar da hare-haren nata, Trump ya ce zai iya gurgunta tattalin arzikin Turkiyya. Kwamitin sulhu na Majalisar Dininkin Duniya za ta yi zaman gaggawa kan janye dakarun Amirka a Arewa maso gabashin Siriya, matakin da kasashen duniya ke Allah wadai.