1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soki Trump kan sadudarsa a gaban Putin

Gazali Abdou Tasawa
July 19, 2018

Wasu manyan 'yan siyasa a Amirka sun soki lamirin Shugaba Donald Trump dangane da yadda ya saduda a gaban Shugaba Vladimir Putin na Rasha a ganawar da suka yi a birnin Helsinki.

https://p.dw.com/p/31Za9
Finnland Helsinki PK Treffen Trump Putin
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Metzel

Wasu manyan 'yan siyasar kasar Amirka sun soki lamirin Shugaba Donald Trump dangane da dadin kan da ya nuna wa Shugaba Vladimir Putin na Rasha a ganawar da suka yi a birnin Helsinki a daidai lokacin da 'yan kasar ta Amirka ke jiran su ga ya bayyana wa Shugaba Putin rashin amincewarsa da katsalandan din da Rasha ta yi a zaben shugaban kasa na 2016. 

Hatta daga bangaren jam'iyyarsa ta Republicain Shugaba Trump ya fuskanci suka da kakkausan lafazi inda alal misali John McCain daya daga cikin shika-shiken jam'iyyar ya bayyana kalaman da shugaba Trump ya yi a gaban Shugaba Putin a lokacin ganawar tasu, da kasancewa abin kasakanci mafi girma da wani shugaban Amirka ya taba yi a gaban shugaban wata kasa a tsawon tarihi. 

A ganawar tasu dai, Shugaba Putin ya musanta zargin yin katsalandan a harakokin zaben kasar ta Amirka na 2016, kuma shgaba Trump ya goya masa baya tare ma da bayyana shi a matsayin wani gwarzo, tare ma da bayyana bukatar bude sabon babin hulda tsakanin kasashen biyu.