1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Trump: Babu ja da baya wajen korar baki idan na lashe zabe

Abdourahamane Hassane MAB
August 13, 2024

A wata tattaunawa da attajiri Elon Musk a kafar sada zumunta ta X, dan takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar Republican Donald Trump ya yi gargadin cewar zai kori baki idan ya samu nasara a zaben watan Nuwamban 2024.

https://p.dw.com/p/4jPh8
Donald Trump a lokacin da yake tattaunawa da Elon Musk a kafar X
Donald Trump a lokacin da yake tattaunawa da Elon Musk a kafar XHoto: Margo Martin via REUTERS

An  fara yin jinkiri na fiye da mintuna 40 kafin a fara tattaunawar saboda matsalolin fasaha da attajiri Elon Musk ya fuskanta, wanda ya ambata a matsayin harin yanar gizo. Shugaban kanfanin sada zumunta na X ya yi magana game da babban harin "DDOS", wanda aka yi niyyar kaiwa don kawo tangarda ga kamfanin don haifar da matsala gabannin tattauna da Donald Trump. Dama  'yan sa'o'i kafin muhawarar, baban kwamishina na sabbin fusahohin zamani na Turai Thierry Breton ya gargadi Elon Musk, yana cewar ya kamata a samar da daidaito a tattaunawar.

Karin bayani: Republican: Ta tabbata Trump ne dan takara

Symbolbild I Wahlen USA -  Trump und Harris
Hoto: Michael Bihlmayer/CHROMORANGE/picture alliance

Tsohon shugaban Amurka Trump ya sake yin alkawarin daukar matakin korar baki mafi girma a tarihin Amurka, yana mai da'awar cewar gwamnatin Biden ta kawo karuwar masu aikata laifuka sabanin yadda lokacin da ya yi mulki. Ya ce: " Zan faɗi yadda alkaluma suka yi kyau, misali a Bulter da ke da girma, amma a cikin lokaci kalilan muka daidaita al' amura na rage yawan baki. Sannan kuma za mu gina katanga tsakaninmu da Mexiko domin hana kwararar baki."

Tsawon sa'o'i biyu, attajiran biyu sun bayyana kamar wasu ƴan uwan ​​juna biyu suna hira a cikin wani "bistro", ba tare da sun nuna taba wata adawa a baya ba. Mista Trump ga misali, ya yi dariya tare da yin suka a kan takarar Kamala Harris wacce ya ce ba ta da azanci duk da cewa hasashen baya bayan nan ya nuna cewar ita ce ke gabansa wajen samun nasara a zaben 2024. Donal Trump ya kara da cewar: "Kamar wannan tattaunawa da muke yi, Kamala ba za ta iya wannan tattaunawar ba. Ba za ta iya ba saboda ba ta da wayo. Ka san ba ta da nitsuwa ."

Karin bayani: EU: Martani kan janyewar Biden daga takara

Trump & Elon Musk X.com Space
Hoto: Andre M. Chang/Zuma/Imago

Mista Trump ya yi amfani da wannan damar wajen bayyana alakarsa da shugabannin kama-karya kamar shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da Kim Jong Un na Koriya ta Arewa, inda ya bayyana cedwar idan ya koma kan karagar mulkin Amurka, kasarsa za ta kasance cikin aminci a fagen duniya. Ya ce: " Na san Putin, na san Shugaba Xi, na san Kim Jong Un na Koriya ta Arewa. Na san kowane, kuma bari in gaya muku, shugabanni ne masu kishin kasashensu wadanda suka tsare kasahensu."

Karin bayani:Kamala Harris na samun goyon bayan 'yan Democrat

Sama da mutane miliyan daya ne suka saurara ko suka kalli hirar kai tsaye a kafar X inda wani lokacin aka soke shafin Donald Trump  bayan harin da magoya bayansa suka kai a kan majalisar dokokin Amurka a shekara ta 2021.