1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Transparency: Koma baya a yaki da cin hanci a Nijar

Gazali Abdou Tasawa
October 15, 2024

A Jamhuriyar Nijar kungiyar transparancy International ta bayyana damuwa kan koma bayan da kasar ke fuskanta a fannin yaki da cin hanci da rashawa da ma kuma yaki da ta'addanci.

https://p.dw.com/p/4lq9u
Shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani
Shugaban Nijar Janar Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

A cikin wani rahoto da ta fitar kan yadda yanayin mulki ke gudana a kasar Nijar a fannoni daban dabam sama da shekara daya bayan juyin mulki kungiyar Transparency International ta nuna damuwa da koma bayan da ake samu wajen yaki da cin hanci da kuma yaki da ta'addanci a kasar ta Nijar. Sai dai wasu 'yan kasar musamman masu goyon bayan mulkin soja na cewa kungiyar ta Transparency International ba ta yi wa hukumomin mulkin sojan kasar adalci ba.

A cikin rahoton mai shafuka 37 kungiyar ta Transparency International ta yi bitar yadda hukumomin mulkin sojan Nijar suka tafiyar da mulki a kasar tare da bayyana irin matsalolin da ta lura kasar na fama da su a tsawon watanni 15 na mulkin sojan da ta ce na bukatar sake dubawa idan har mahukuntan na son cimma buri da kuma fatan da 'yan Nijar. Batun yaki da cin hanci da rashawa wanda ke sahun gaba a ayyukan da sabbin hukumomin mulkin sojan suka yi ikirarin za su yi na daga abubuwan da kasar ta fuskanci koma baya a karkashin mulkin sojojin a cewar Malam Maman Wada shugaban kungiiyar ta Tarnsparency reshen Nijar.

Shugaban Nijar Janar Abdourahmane Tiani
Hoto: Balima Boureima/Reuters

"Sojoji da suka dauki iko ba su tunkarin cin hanci da rashawa ba. Sai kawai suka yi wata kungiya da suke ce wa COLDEF. aikinta karbo kudi wajen wadanda ake zargin sun yi handama. In an tuhumi mutum kamar ya ci kudi miliyan 100, shi ke nan ana iya gyara wa babu zuwa kotu babu yin kaso. Karin karawa sai shugaban kasa ya dauki wata doka wacce ta ce duk kudin da za a kashe a fannin tsaro da ayyukan gine gine a gidan shugaban kasa da fadarsa, babu izinin a yi bincike. Wannan yana nufin cin hanci da rashawa an mayar da shi baya"

Kazalika kungiyar ta Transparancy International ta ce hatta batun da ‘yan kasa suka yi fatan mulkin sojan zai magance kusan ba abin da ya sauya a cikin watanni 15 a cewar rahoton.

Baraden yaki da ta'addanci a Nijar
Baraden yaki da ta'addanci a NijarHoto: Gazali Abdou Tasawa/DW

"Matsalar tsaro ta zama a yanzu babu ma inda babu ta'addancin a cikin kasa. Kuma duk manyan sojoji da suka kware a fannin yaki da ta'addanci, an nada su manyan daraktocin manyan kamfanonin kasa inda ake shan sanyi ana samun kudi da motoci masu kyau. An bar kanana suna ganin arkane a fagen daga. Akwai inda talakawa da kansu suke neman makamai su kwari da baka suna kare kansu. Akwai wuraren da idan an dauki dabbobi ko an kira jami'an tsaro ba sa zuwa saboda basu da yawa ko kuma basu da makamai. Sai dai talakawa ko dai su shiga masallaci su roki Allah ko kuma su tsaya a yi abin da aka ga dama da su"

Rahoton kungiyar ta Transparency ya kuma nuna damuwa kan yadda matakin jingine jam'iyyun siyasa tun bayan juyin mulki ke hana hatta shugabanni siyasar kasar iya yin tsokaci kan lamurran da ba sa tafiya daidai a kasar. Sai dai Malam Ibrahim Namaiwa na kungiyar M62 da ke goyon bayan mulkin soja a Nijar na ganin zargin da rahoton ya yi ba gaskiya ba ne.

Firaministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine
Hoto: Balima Boureima/Anadolu Agency/picture alliance

"Shi yaki da cin hanci da rashawa kowa ya san ba matsala ba ce wadda za a iya tashi loakci daya a magance ta. Amma a yau cikin wannan mulki na soja kowa ya ga irin matakan da ake dauka na yaki da cin hanci. A yaki da ta'addanci ma, kowa yana gani duk safiya ta Allah a daji da garuruwa jami'an tsaro masu yaki da ta'addanci. Kuma kullum ana jin labarin cewa jami'an tsaro sun kai hari sun halaka 'yan ta'adda"

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin kasar ta Nijar ba ta ce uffan ba a game da wannan rahoto wanda ba shi ne na farko ba da kungiyar ta Transparency Intenational ke fitarwa na sukar lamirin yadda sojoji ke tafiyar da mulki a kasar. Sai dai wasu 'yan Nijar na zargin kungiyar ta Transparency International na rawa ne da bazar wasu kasashe da kungiyoyin duniya masu adawa da mulkin sojan kasar da ke fakewa ga guzuma don su harbi karsana.