1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS na kokarin sasanta siyasar Togo

Gazali Abdou Tasawa AA/SB
September 10, 2018

A wannan Litinin ce masu sa ido na kungiyar ECOWAS ko CEDEAO suka isa birnin Lome a kasar Togo da nufin sasanta bangarorin siyarar kasar na ´yan adawa da masu mulki kan batun jadawalin zabukan kasar.

https://p.dw.com/p/34cHi
Proteste in Togo gegen Gnassingbe ARCHIV
´Yan adawa na zanga-zanga a TogoHoto: picture alliance/AA/ Alphonse Ken Logo

Watanni da dama kenan dai da kawancen jam'iyyu 14 a adawa na kasar ta Togo ke nuna rashin amincewarsu da tsarin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar, tare da kin aikawa da wakillansu. Kawancen jam'iyyun dai na neman ganin an sake fasalin hukumar zaben tare da kara wa bangaran 'yan adawa wakillai, idan har ana so su shiga zabe mai zuwa na ran 20 ga watan Disamba kamar yadda jaddawalin kungiyar Ecowas ya tanadar. Sai dai wasu masu lura da harakokin siyasar kasar ta Togo na zargin 'yan adawar kasar, da rashin sassauci ga shawarwarin da ake gabatar masu na neman sasanta rikicin siyasar kasar. Sai dai Brijitte Adjamagbo jagorar kawancan jam'iyyun adawar kasar ta yi fatali da wannan zargi:

ECOWAS und Präsident Faure Gnassingbe
Shugaba Faure Gnassingbe na Togo lokacin yana shugabancin ECOWASHoto: picture-alliance/ dpa/dpaweb

"Na yi mamaki da wannan zargi da ake yi mana na rashin sassauci, ni ban ga a kan wata hujja ba za a zargemu da wannan. Domin a shirye muke mu hau tebirin tattaunawa da kowa domin ganon bakin zaren warware wannan sabani ta yadda za mu iya cimma matsaya guda kan wannan jadawali na zabe, ba tare da mun yi watsi da manufofin da muke kokarin karewa ba. A shirye muke mu yi sassauci amma wannan ba ya nufin cewa za mu amince mu yi watsi da komai ba."

Brijitte Adjamagbo ta kara da cewa, akwai wasu batutuwa da jaddawalin da Kungiyar ECOWAS ta tanada na zuwa zaben da ke bukatar a sake zama domin fahimtar ma'anarsu tsakanin bangarorin siyasar kasar wanda kowa ke fassarawa a bisa yadda ya ga tana gyarashi. Kuma shi ma daga nashi bangare Akbishop Pierre Chanel Affognon shugaban kawancan kungiyoyin farar hula na "Esperance pour le Togo" na ganin mafita daya a cikin wannan rikici, ita ce ta aiwatar da shawarwarin da kungiyar ta CEDEAO ta fitar:

Togo Präsidentschaftswahlen
Shugaba Faure Gnassingbe na TogoHoto: I. Sanogo/AFP/Getty Images

"A cikin kundin shawarwarin na Ecowas akwai abubuwa masu muhimmanci kuma na alkhairi, Muna so mu ga an aiwatar da su, ba ma son a jefasu karkashin tebur a manta da su"

A farkon watan Agustan da ya gabata dai kawancan jam'iyyun adawar kasar ta Togo ya yi watsi da shawarwarin da shugabannin kasashen ECOWAS suka fitar da suka hada da shirya zabuka kafin karshen wannan shekara ta 2018, suna masu zargin shugabannin na ECOWAS da kin fitowa fili su bayyana matsayinsu kan batun da ya fi ci wa 'yan adawar tuwo a kwarya kan nacewar da shugaba Faure Gnassingbe ke yi ta neman sake tsayawa takara a karo na hudu a zaben shekara ta 2020 alhali dokokin kungiyar ta CEDEAO ta takaice mulkin shugabannin kasashen a wa'adi biyu kawai.

Yanzu dai 'yan kasar ta Togo sun zura idanu su ga tasirin da zuwan tawagar masu shiga tsakanin zai yi wajen kawo karshen rikicin siyasar da ya ki ci ya ki cinyewa watanni da dama.