1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa na Togo ya dauki sabon salo

Abdourahamane Hassane SB
December 7, 2018

A kasar Togo da ke yankin yammacin Afrika an kadammar da yakin neman zabe na 'yan majalisun dokoki da za a yi ranar 20 ga wannan wata na Disamba. Sai dai kuma 'yan adawa na kasar sun ce ba za su halarci zaben ba.

https://p.dw.com/p/39e4P
Togo Demonstrationen
Hoto: DW/N. Tadegnon

Hadin gwiwar jamiyyun siyasar Togo su 14 sun yi amfani da wannan rana domin kiran yajin aiki na gama gari wato "Togo mort" a duk fadin kasar domin nuna rashin jin dadi kan halin rashin kula da bukatar da suka gabatar wa gwamnati na sake nada mambobin hukumar zaben kasar da ake kira CENI. Kafui Adjamagbo-Johnson ta ce gwamnatin Shugaba Faure Gnassingbé ba ta da niyyar neman hanyoyin sasantawa da 'yan adawar domin tana son ta yi tarzace ba kuma za a yarda ba.

Wannan kai ruwa rana da aka shiga tsakanin gwamnatin da 'yan adawa sama da shekara, ya janyo tsaiko wajen tafiyar tattalin azikin kasar ta Togo wanda dama ke da rauni, wasu daga cikin 'yan kasar ta Togo dai na dora gaza warware rikicin a kan kungiyar ECOWAS ta kasahen yammacin Afirka.

A halin da ake ciki dai gwamnatin ta Togo ta haramta duk wata zanga-zanga ta 'yan adawar a lokacin da ake gudanar da yakin neman zabe na 'yan majalisar dokoki wanda za a yi a ranar 20 ga wannan watan na Disamba. Tun farko dai kungiyoyin malaman cocin sun bukaci da a dage zaben domin samun masalaha tsakanin gwmnati da 'yan adawar sai dai kuma babu alamun gwamnatin za ta saurara musu