1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mulki ba tare da firaminista ba a Togo

July 12, 2024

Shugaban Togo Faure Gnassingbé na ci gaba da jan ragar mulki kasarsa ba tare da kafa gwamnati ba, tun bayan murabus da tsohuwar gwamnati ta yi kusan watanni biyun da suka gabata.

https://p.dw.com/p/4iEtj
Togo | Shugaban Kasa | Faure Gnassingbé
Shugaban kasar Togo Faure GnassingbéHoto: Filip Singer/EPA POOL/dpa/picture alliance

Ana dai bayyana matakin na Shugaba Faure Gnassingbé na Togo da karan-tsaye ga tsarin mulki da ba ya rasa nasaba da matsalar da fadar mulki ta Lomé ke fuskanta wajen neman kafa salon mulkin da majalisar dokoki ke sa ido a kai, kamar yadda sabon kundin tsarin mulkin kasar ya tanada. A ranar 21 ga Mayun wannan shekara ta 2024 ne gwamnatin Victoire Dogbé ta yi murabus, domin bai wa shugban kasar Togo damar aiwatar da muhimmin sashe na kundin tsarin mulkin kasar da ya tanadi mulkin firmainista mai karfin fada a ji. Wannan yana nufin cewar kasar ta yammacin Afirka na tafiya tsawon makonni bakwai, ba tare da sabon firaminista da kuma sauran ministaoci da ke aiwatar da sassa na dokokin kasar ba. Sai dai dan jarida Tchaboré Bouaima ya ce babu dalilin damuwa kan rashin sabuwar gwamnati a Togo, domin har yanzu tsofaffin ministocin gudanar da ayyukan yau da kullum da ke aikin rikon kwarya a ma'aikatunsu. Amma dai yanayin siyasar Togo ya saba da wasu kasashe na duniya, domin mulkin dan da ya gaji ubansa ake a wannan kasa. Sannan Shugaba Gnassingbé ya kwaskware kundin tsarin mulki, domin samun damar yin tazarce.

Togo | Zabe | Majalisar Dokoki
Jam'iyyar Shugaba Faure Gnassingbé na Togo ce, ta lashe zaben 'yan majalisun dokokiHoto: Emile Kouton/AFP

Sai dai masanin kimiyyar siyasa Mohamed Madi Diabakaté ya ce akwai kwakkwarar hujja da ke sa shugban kasa jan-kafa wajen kafa sabuwar gwamnatin, wanda ba wani abu ba ne illa halin rikon kwarya da ake ciki. Sabon kundin tsarin mulkin Togo ya sa kasar tashi daga tsarin mulkin shugaban kasa mai cikakken iko, zuwa ga tsarin majalisar dokoki mai karfin sa-ido kan duk wani kai kawo na gwamnati. Saboda haka ne masanin dokoki Tchaboré Bouaima ya ce sabon kundin tsarin mulkin, ya tanadi wa'adin rikon kwarya kafin sababbin ma'aikatu da cibiyoyin gwannati su fara aiki. Mohamed Madi Diabakaté da ke zama masanin siyasar Togo yana da yakinin cewa, shugaban kasa Faure Gnassingbé zai dauki lokaci kafin ya kafa dukkanin sababbin hukumomi tare da nada shugaban gwamnati. Kawo yanzu dai babu wani bayani kan ranar gudanar da zaben sabon firaministan, wanda a tsarin Togo ake kira shugaban majalisar ministoci. Amma sabon kundin tsarin mulki kasar ya tanadi cewa, shugaban jam'iyyar da ke da rinjaye a majalisa ne ya kamata ya rike wannan mukami. Idan za a iya tunawa dai jam'iyyar shugaban kasar ce  ta samu wannan matsayi, a  lokacin zaben 'yan majalisa da ya gudana a watan Afrilun 2024.