1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hare-hare 'yan ta'adda ya kashe mutane 30 a Togo

Zainab Mohammed Abubakar
November 28, 2023

A wata sanarwa da ba kasafai ake ji ba kan harkokin tsaro, gwamnatin Togo ta ce, hare-haren ‘yan ta’adda a arewacin kasar ya kashe mutane fiye da 30 a cikin wannan shekara.

https://p.dw.com/p/4ZXCN
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Kasashen Togo da Benin da Ghana da kuma Cote'd Voire, dukkansu makwabta a mashigin tekun Guinea, suna fuskantar barazanar karuwar tashe-tashen hankula daga rigingimun masu jihadi daga kan iyakokin Nijar da Burkina Faso.

Ministan sadarwa na Togo Yawa Kouigan, ya shaidawa gidan talabijin din kasar ta TVT cewa mutane 31 ne suka mutu, 29 kuma suka jikkata, yayin da wasu uku suka bace bayan aukuwar rikicin da ke dangantawa da 'yan ta'adda.

Kakakin na gwamnati ya ce, kasar ta fuskanci harin kwanton bauna da fadace-fadace 11 da kungiyoyin 'yan ta'adda masu dauke da makamai da kuma da kuma, yawan fashe fashen abubuwa masu nasaba da bama-bamai.