1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Togo da Kamaru sun dau hankalin jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal
February 21, 2020

Zaben shugaban kasa a Togo da rikicin 'yan awaren Kamaru da bullar farin dango a gabashin Afirka sun dau hankalin jaridun Jamus a wannan mako.

https://p.dw.com/p/3Y8aR
Wahllokal in Togo
Hoto: DW/N. Tadégnon

Jaridar Die Tageszeitung ta yi tsokaci kan zaben shugaban kasar Togo na ranar Asabar tana mai cewa iyalin wani gida ke tafiyar da harkokin mulki tsawon shekara da shekaru a kasar ta Togo da ke yankin yammacin Afirka babu kuma mai imanin cewa za a samu sauyi hatta su kansu 'yan adawa. Jaridar ta ce shugaban kasa Faure Gnassingbe mai shekaru 53 da tun a 2005 yake shugabancin kasar bayan mutuwar mahaifinsa, Gnassingbe Eyadema da tun a 1967 ya tafiyar da wani mulki na kama karya, ya mamaye yakin neman zabe a tsakanin mutum bakwai da ke takarar shugaban kasa. Jaridar ta ce a baya-bayan nan mutane na takatsantsa wajen yin wata magana game da iyalin na Gnassingbe. 

Kamerun Präsident Paul Biya
Hoto: picture-alliance/Photoshot/Ju Peng

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung ta leka kasar Kamaru ne a wani labari da ta buga mai taken cin zarafi maimakon ba da ilimi. Ta ce a Kamaru malamai da yara 'yan makaranta na fuskantar barazana daga 'yan aware inda masu tada kayaar bayan ke garkuwa da mutane a wasu lokutan ma su hallaka su. Jaridar ta ce rikici tsakanin yankin masu magana da harshen Ingilishi na Kamaru da gwamnatin tsakiya mai amfani da harshen Faransanci ya yi muni fiye da yadda ake zato. Ta ce abin takaici shi ne rikicin ya fi shafar makarantu a lardin yammacin kasar, inda yanzu haka an rufe da yawa daga cikin makarantun, musamman a birnin Bamenda da ke zama babban birnin Jihar Arewa maso Yamma.

Jemen Sanaa | Wüstenheuschrecken
Hoto: DW/Y. Safia Mahdi

Farin Dango na ta'adi a gabashin Afirka wannan shi ne taken labarin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta buga gama da annobar Farin Dango da ke cinye albarkatun noma a wasu kasashen na yankin gabashin Afirka. Ta ce tun wasu makonni da suka wuce halin da ake ciki a gabashin Afirka ya ta'azzara bayan da Farin Dango suka mamaye gonaki a kasashen Kenya, Habasha da kuma Somaliya, yanzu kuma sun isa kasashen Yuganda da Tanzaniya. Jaridar ta ce girmar ayari daya na farin ya kai murabba'in kilomita 2400, kuma cikin sauri suna cinye ko kuma suna lalata albarkatun noma.