1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taɓarɓarewar al'amuran tsaro a Burundi

September 20, 2011

Hare haren da ake kai wa a ƙasar Burundi na barazanar' sake saka ƙasar cikin wani hali na rashin kwanciyar hankali

https://p.dw.com/p/12d5i
Shugaban ƙasar Burundi Pierre Nkurunziza, ya ziyarci gawarwarkin mutanen da aka kashe a hare harenHoto: dapd

A ƙasar Burundi yanzu haka ana ci- gaba da zaman ɗarɗar bayan da wasu mutanen da ba a shaidda ko su wanene ba suka kai wasu hare hare a jiya a cikin wani wurin sayar da barasa da ke a garin Gatumba kusa da Bujumbura babban birnin ƙasar inda suka kashe mutane,wannan ya sa an shiga fargaban sake ɓarkewar wasu sabbin tashe tashen hankula bayan yaƙin basasar da aka yi fama da shi shekaru shida da suka wucce.

Ƙasar ta Burundi ta samun zaman lafiya ne da ƙwanciyar hankali tun a shekara ta 2005 lokacin da yan tawayen hutu na ƙungiyar FNL suka ajiye makamai kana kuma suka shiga cikin gwamnatin bayan tsawon shekaru gomai da aka ƙwashe ana fama da yaƙe yaƙen basasa a ƙasar.To sai dai a cikin watannin baya baya nan judu alaina ake fuskantar hare hare tun bayan bayan zaɓbuɓukan da aka gudanar a shekara bara wanda yan' adawar suka ƙauracewa saboda zargin tabƙa magudi kafin ma a gudanar da zaɓen.

Galibi dai yawancin yan adawar na ƙasar sun fuce zuwa ƙasar RDC inda suke yi gudun hijira, kuma ko da shi ke yazuwa yanzu ya na da wahala a ce wata sabuwar tawaye ce ke ɓulo wa a ƙasar ,amma harin da aka kai a mashayar ta garin Gatumba wanda shaiddun garin suka tabatar da cewa galibi magoya bayan jamiyar da ke yin mulki ta shugaba Pierre Nkurunziza ;sune ke hole wa a gurin ya sa ana zaton wani abu mai kama da hakaJunior Biraronderwa menba ne a cikin wata ƙungiya ta matasa da ake kira da sunan FRODEBU''ya ce mun yi kira ga shugaban ƙasa wanda shi ne mutumi na farko da ya kamata ya kiyaye tsaro al'umma ya ɗauki matakan da suka dace domin dakatar da kashe kashen jama'ar da ake yi;ya ce kuma muna kira ga ɗaukacin hukumomin ƙasar da su tabata da tsaro na kiyaye lafiyar al umma da dukiyoyin su.

Yawanci dai shaidu wanda suka tsira daga harin da aka kai na garin Gatumba sun ce waɗanda suka farma su suna sanye ne da kayan yan sanda kana kuma ɗauke da wuƙake da kuma bindigoki.Jagoran dai ta kungiyar yan tawyen Agathon Rwasa wanda ke yin gudun hijira a a RDC ya ce ba su da hannu a hare haren .To sai dai wanin jamin ƙungiyar CRISIS Group wacce ke yin riga kafiga kafi ga aukuwar tashe tashe hankula da kuma dorewar demokaraɗiyya Thierry Vircoulon ya ce ba za a iya samun zaman lafiya a ƙasar ta Burindi ba matuƙar gwamnatin na ci gaba da nuna wa yan adawa wariya waɗanda galibi suke yin hijira a ƙasashen waje.

A ƙasa za a iya sauraron sautin wannan rahoto

Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi