1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddamar yankin Abiyei na kudancin Sudan

June 4, 2011

Majalisar Ɗinkin Duniya na ƙara matsin ƙaimi a kan gwamnati a Khartoum da ta janye dakarunta a iyakar da ke tsakanin kudanci da arewacin Sudan.

https://p.dw.com/p/11UHA
Shugabannin Sudan, Salva Kiir da Omar Al-BashirHoto: picture-alliance/dpa

Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kakkausar suka ga gwamnatin Sudan, sakamakon baza dakarun sojojinta da ta yi a yankin Abiyei mai arziƙin man fetur, inda kuma gwamnatocin arewaci da kudancin ƙasar ke taƙaddamar wanda zai ɗora hannu a kai.

Wannan mamaya da gwamnatin ta Sudan ta yi a yankin Abiyei, ya kai ga ficewar dubunnan fararen hula sakamakon rashin matsugunen su. Ita dai gwamnati a Khartoum, ta aika da dakarunta zuwa kudancin Sudan ne a ran 21 ga watan Mayun da ya gabata, inda suka ƙona gidaje suka kuma lalata dukiyar fararen hular yankin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce aƙalla mutane dubu 60 sun fice daga yankin. Wata sanarwa da kwamitin ƙolin Majalisar Ɗinkin Duniyar ya fitar, ya ce matakin da gwamnatin ta Sudan ta ɗauka ya saɓawa yarjejeniyar sulhun shekarar 2005 wacce ta kawo ƙarshen yaƙin basasar ƙasar.

Har yanzu dai ba'a kai ga cimma wata matsaya dangane da makomar yankin na Abiyei ba, abun da ke da muhimmanci ga kudancin ƙasar a yayin da take shirin gudanar da bukin samun 'yancin kai a ranar tara ga watan Yuli mai zuwa.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal