1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddamar yankin Abiyei a Sudan

May 23, 2011

Mallakar yankin Abiyei na ci-gaba da haifar da taƙaddama tsakanin Arewaci da Kudancin Sudan tun bayan da ƙasar ta jefa ƙuri'ar raba gardama

https://p.dw.com/p/11LpB

Tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya a Sudan ta yi kira ga gwamnatin ƙasar da ta janye dakarun ta daga yankin Abiyei mai arziƙin mai, wadda arewaci da kudancin Sudan suke taƙaddama a kai. A wata sanarwar da majalisar ta fitar a Khartoum babban birnin Sudan, Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna matuƙar damuwar sa bisa taɓarɓarewar da taƙaddamar ke yi tsakanin ɓangarorin biyu. Babbar jami'ar da ke kula da harkokin wajen EU, Catherine Ashton ta yi Allah wadai da tashe-tashen hankulan kuma ta yi kira ga gwamnati a Khartoum da ta janye dakarun ta daga yankin ba tare da ɓata lokaci ba. A ƙarshen makon da ya gabata, dakarun arewacin Sudan suka mamaye yankin na Abiyei wanda ke iyakar ta da yankin kudancin da ke gab da bikin 'yancin kai.

Wani mawallafi kuma ƙwararre kan al'amurar Sudan, ɗan asalin Burtaniya Douglas Johnson, ya ce za'a iya shawo kan wannan taƙaddama idan yankin Abiyei  ya kafa nasa gwamnatin kamar yadda yarjejeniyar sulhun ta tanadar tun farko:

"za'a iya shawo kan duk wannan idan har aka aiwatar da yarjejeniyar da ɓangarorin suka riga suka rattabawa hannu da kuma dokar ƙuri'ar raba gardama, wadda ke bada damar tantance waɗanda zasu iya kaɗa ƙuri'a a zaɓen raba gardamar."

Ana sa ran dai kwamitin sulhun MDD zai gudanar da tattaunawar sulhu a Khartoum dangane da wannan batun.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Muhammad Nasiru Awal