1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama a tsakanin Sudan da Sudan Ta Kudu

March 2, 2012

Sabon rikicin da ya ɓarke a tsakanin Sudan da Sudan Ta Kudu ya janyo zubar da jini da kuma kakkausar martani daga ɓangarorin guda biyu.

https://p.dw.com/p/14D7h
(FILE) A file picture dated 19 January 2010 shows Sudanese President Omar el Bashir (R) and First Vice President and President of the Government of Southern Sudan, Salva Kiir Mayardit (L), participating in celebrations marking the 5th anniversary of the signing of the Comprehensive Peace Agreement (CPA) in Yambio, Sudan. Omar el Bashir has won the country's first multiparty elections in 24 years, election officials said on 26 April 2010. The polls are supposed to usher in a new era of democracy in Sudan, which is recovering from a decades-long civil war between the north and south. EPA/TIM MCKULKA - UNMIS - HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++
Omar el Bashir da Salva Kiir MayarditHoto: picture-alliance/dpa

Hukumomin ƙasar Sudan sun yi barazanar ɗaukar fansa bayan da sojojin Sudan ta kudu suka kashe dakarunta su 150. Hakan dai na zuwa ne bayan da gwamanti a birnin Khartoum ta musanta zargin da mahukuntan birnin Juba suka yi cewa jiragen saman rundunar sojin Sudan sun kai harin bama-bamai akan rijiyoyinta na man fetur da ke kusa da iyakar kasashen biyu da suke gaba da juna. Mohammad Nasiru Awal na ɗauke da ci-gaban rahoton.

Ministan watsa labaran Sudan ta kudu Barnaba Marial Benjamin da ya yi Allah wadai da abin da ya kira takalar fada ta Sudan, ya ce bama-bamai sun lalata wata cibiya ta samar da ruwan sha ga ƙasarsa a Ƙordofan ta kudu. Dama dai ƙasashen biyu na taƙaddama game da wanda ya mallaki wannan yanki mai arziƙin man fetur. Sudan da kuma Sudan ta kudu na zargin junansu da ɗaure wa 'yan tawayen ƙasashen na su gindi da nufin haddasa ruɗu a ƙasashen nasu.

Hakan dai na zuwa ne bayan da gwamnati a birnin Juba ta ce a shirye ta ke ta ɗau fansa sannan ta jaddada cewa mamaye garin Jaw mai muhimmanci dake kan iyakarta ba bisa ƙa'ida ba da Sudan ta Arewa ta yi, ya janyo kashe sojojin ta su kimanin 150. Gwamnatin Sudan Ta Kudu ta ce ta na da 'yancin kashe sojojin Sudan ta arewa saboda kutsen da suka yi mata tare da mamaye garin na Jaw tsawon watanni uku.

An oil worker turns a spigot at an oil processing facility in Palouge oil field in Upper Nile state February 21, 2012, following a dispute with Sudan over transit fees. South Sudan will refuse do to any business in the future with oil trader Trafigura if it is proven that the firm bought oil from neighbouring Sudan in the knowledge that the cargo was seized southern crude, its oil minister told Reuters. Picture taken February 21, 2012. REUTERS/Hereward Holland (SOUTH SUDAN - Tags: ENERGY POLITICS BUSINESS)
Hoto: Reuters

Sudan ta ce ba ita ce ke da laifi ba

A nata ɓangaren Sudan na zargin makwabciyarta da shiga yankinta ba bisa ƙa'ida ba sannan kakakin gwamnatin Sudan Hassan Ali Osman ya zargi Sudan ta kudu da taimakawa 'yan tawayen ƙungiyar Sudan Revolutionary Front da ta lashi takobin kifar da gwamnatin shugaba Omar Hassan El Bashir.

"Suna goya wa 'yan tawayen Ƙordofan Ta Kudu baya. Kai suna ma taimakawa 'yan tawayen lardin Darfur."

Darfur dake yammacin Sudan Ta Arewa, cibiyar 'yan tawaye ƙungiyar Justice and Equality Movement ne. A lokacin da yake tsokaci ga barazanar da Sudan ta arewa ta yi na kai hari kan Sudan Ta Kudu, Agina Ojwang masani a yankin ya ce akwai wasu dalilai na ɓoye:

"Sudan Ta Arewa na son ta mamaye Sudan Ta Kudu domin ƙaddamar da yaƙi da za ta yi amfani da shi domin karkata hankulan al'ummarta. Sannan tana ƙoƙarin samun goyon bayan larabawar arewa domin haɗa kai a yaƙi da gwamnatin kudu. Tun da daɗewa gwamnatin Khartoum ke shirya wannan maƙarƙashiya. Yanzu haka Sudan Ta Arewa na fama da matsalolin tattalin arziƙi saboda asarar kuɗaɗen shiga daga man fetur."

Southern Sudanese soldiers deployed to provide security during an independence rehearsal procession in Juba, southern Sudan on Thursday, July 7, 2011. The Government of Southern Sudan is making lavish preparations to celebrate its declaration of independence from the north on Saturday, July 9th. The south's secession comes after decades of brutal civil war between north and south that resulted in more than two million deaths, most of which were southerners. (ddp images/AP Photo/Pete Muller)
Hoto: AP

Tushen Rikicin baya bayannan a tsakanin Sudan da Sudan Ta Kudu

Tun fiye da watanni biyu kenan da aka rufe bututun tura mai zuwa arewacin Sudan bayan da Sudan Ta Kudu ta zargi gwamnatin Khartoum da sata mata mai dake ratsawa ta ƙasar zuwa kasuwannin ƙasa da ƙasa.

A halin da ake ciki Amirka  ta zargi shugaba Omar al-Bashir na Sudan da hana ruwa gudu a ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya tsakanin ƙasarsa da kuma Sudan Ta Kudu. Sakatariyar harkokin wajen ƙasar ta Amirka wato Hilary Clinton ta bayyana wa majalisar dokokin ƙasarta cewa shugaban Sudan na ƙoƙarin yin ƙafar Ungulu ga yarjejeniyar sulhun da ƙasarsa ta ƙulla da Sudan Ta Kudu.

Mawallafi : Mohammad Nasiru Awal
Edita : Saleh Umar Saleh