1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama a tsakanin Rasha da NATO

July 5, 2011

Ana ci gaba da samun rarrabuwar kawuna a tsakanin Rasha da NATO akan batun rikicin Libiya

https://p.dw.com/p/11p0T
Hagu zuwa dama: Rasmussen da Sergei Lavrov da kuma Guido WesterwelleHoto: picture alliance/dpa

Wani taron ƙolin daya gudana a tsakanin Rasha da ƙungiyar ƙawncen tsaron NATO ya kammala ba tare da dukkan sassan biyu sun cimma dai dai to akan batun rikicin ƙasar Libiya ba. A lokacin taron, wanda ya gudana a birnin Sochi - dake tekun Bahr al-Aswad, ministan kula da harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya zargi ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO da wuce gona da iri wajen fassara ƙudirin da kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya zartar akan Libiya. Hakanan ƙasar ta Rasha ta yi Allah wadai ga matakin da Faransa ta ɗauka na turawa 'yan tawayen ƙasar ta Libiya manyan makamai.

Sai dai sakatare janar na ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO Anders Fogh Rasmussen ya kare matakan da cewar ana tsananin buƙatar su domin kare fararen hular ƙasar Libiya daga hare-haren da sojojin dake biyayya ga shugaba Mouammer Gadhafi ke kai musu. Hakanan ya kare matakin da NATO ta ɗauka na shirin sanya na'urorin bada kariya daga makamai masu linzami a nahiyar Turai, wanda kuma Rasha ke ɗauka a matsayin barazana ce ga sha'anin tsaron ta:

"Ya ce: Muna son Rasha ta kwana da sanin cewar NATO ba wata barazana bace gare ta, domin kuwa hakan shi ne haƙiƙanin al'amarin."

A halin da ake ciki kuma alƙalumar dake fitowa daga ƙungiyar NATO na nuni da cewar, ta riɓamya irin hare-hare ta jiragen saman da take kaiwa a ƙasar ta Libiya inda take tura jiragen yaƙin da jefa bama-bamai kimanin 71 a cikin sa'oi 24.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu