1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama a kan Kogin Nilu

June 18, 2013

A karon farko Habasha da Masar sun amince su hau teburin tattaunawa dan samun maslaha ga rikicin madatsar ruwan Habasha da ke neman tada zaune tsaye a yankin.

https://p.dw.com/p/18rlj
--- 2013_06_14_nil.psd

Ministocin harkokin wajen ƙasashen Habasha da Masar sun amince su zauna kan teburin tattaunawa dangane da madatsar ruwar da mahukuntan Addis Ababa ke ƙoƙarin ginawa a kan kogin Nilu, domin kashe wutar rikicin da ya fara ruruwa tsakanin ƙasashen biyu, tun bayan da Habasha ta bayyana wannan ƙuduri na ta.

Wannan sanarwa ta zo ne bayan wata ganawa tsakanin ministan harkokin wajen Habasha Tedros Adhanom da takwararsa na Masar Mohammed Kamel Amr bayan da mahukuntan Alƙahira su ka bayyana damuwar cewa madatsar ruwar za ta rage musu wadatar ruwa a ƙasarsu saboda komai ya dogara kan ruwan da su ke samu daga kogin Nilun ne.

Dalilin Habasha na gina madatsar ruwan

Habasha na muradin gina wannan madatsar ruwan ne domin ta samar da wutar lantarkin da za ta iya aikawa ƙasashe maƙota kamarsu Kenya da Djibouti idan har ta cimma wannan buri madatsar ruwan za ta kasance mafi girma duk faɗin Afirka a cikin madatsu irin ta masu samar da wutar lantarki, kuma ta sanya wa'adin shekara ta 2017 dan kammala shi kana kuma duk kuɗaɗen za su fito daga cikin gidanta ne.

Tedros Adhanom ya nuna gamsuwarsa da tattaunawar da suka yi da takwaran aikin na sa na Masar, inda ya ce bangarorin biyu sun ƙaru da musayar batutuwan da suka yi kuma ya karanto sanarwar haɗin gwuiwar da suka fitar a ƙarshen wannan ganawa ta su.

A picture taken on May 28, 2013 shows the Blue Nile in Guba, Ethiopia, during its diversion ceremony. Ethiopia has begun diverting the Blue Nile as part of a giant dam project, officials said on May 29, 2013 risking potential unease from downstream nations Sudan and Egypt. The $4.2 billion (3.2 billion euro) Grand Renaissance Dam hydroelectric project had to divert a short section of the river -- one of two major tributaries to the main Nile -- to allow the main dam wall to be built. 'To build the dam, the natural course must be dry,' said Addis Tadele, spokesman for the Ethiopian Electric Power Corporation (EEPCo), a day after a formal ceremony at the construction site. AFP PHOTO / WILLIAM LLOYD GEORGE (Photo credit should read William Lloyd-George/AFP/Getty Images)
Dam ɗin Habasha da Masar a Kogin NiluHoto: William Lloyd-George/AFP/Getty Images

"Dangane da madatsar ruwan da Habasha ke so ta gina, ministocin biyu sun amince da tanadin shawarwarin kwamitin ƙwararru wanda ya shawarci gudanar da tattaunawa tsakanin Masar, Habasha da Sudan cikin gaggawa, dangane da yadda za su aiwatar da sauran tanade-tanden da suka wajaba, waɗanda suka haɗa da gudanar da cikakken bincike, kuma Habasha ta amince da shawarar da Masar ta bayar na cewa ministocin harkokin waje da na ruwa a ƙasashen uku su fara tattaunawa.

Matakin tabbatar da ci gaba ga wannan batu

Sanarwar ta kuma yi na'am da samun goyon bayan cibiyoyin siyasar ƙasar. A ƙarshen wannan ganawa da ministocin suka yi dai, sun ce za su ƙarfafa dangantakar da ke tsakaninsu su cigaba da tattaunawa su na kuma hulɗa da juna domin su tabbatar sun aiwatar da shawarwarin da suka cimma ko a wannan ganawar ta su, kuma a dalilin haka, ministan harkokin wajen Habasha ya amsa goran gayyatar da ministan harkokin wajen Masar ya miƙa masa, inda ake sa ran zai ziyarci Masar nan ba da daɗewa ba. Ga ma ƙarin bayanin da ministan harkokin wajen Masar ɗin Mohammed Kamel Amr ya bayar.

"Habasha da Masar sun daɗe suna hulɗa da juna, sun shekaru gommai suna aiki tare, kuma insha Allah hakan zai ci gaba, Kogin Nilu wanda ke zaman ƙashin bayan rayuwar ƙasashen biyu musamman ma Masar, wadda ba ta da wani kafar samun ruwa da albarkatunsa banda shi. Na sha faɗin cewa idan babu kogin Nilu, babu Masar, kuma na san cewa 'yan uwanmu na Habasah sun san da haka kuma su na la'akari da shi. Ina sake jaddada cewa mun gudanar da wannan tattaunawa saboda yanayi na hadin kai da na ƙawanace da kuma sha'awar ɗaukar matakin da zai mutunta ƙasashen biyu. Kamata ya yi a ce kogin Nilu ya haɗa mu ba wai ya raba mu ba"

CAIRO, EGYPT - FEBRUARY 14: Cairo couples and families enjoy deboard from a cruise on Nile River at sunset on Valentine's Day, February 14, 2011 in Cairo, Egypt. Although not a traditional holiday in Egypt, globalization has made Valentine's Day increasingly popular with young urban Cairenes. For many Egyptians, life has slowly begun to return to normal, just days after the overthrow of former President Honsi Mubarak. (Photo by John Moore/Getty Images)
Masar-Kogin NiluHoto: Getty Images

Daga farko dai wasu 'yan siyasar Masar sun kaɗa gangunan yaƙi kan wannan madatsar ruwa, to sai dai a makon da ya gabata, shugaban ƙasar Mohammed Mursi, ya ce akwai zaɓi daban-daban kuma ministan harkokin wajen Masar ya ce kalamai marasa daɗin da aka ji a baya an yi su cikin ɓacin rai kuma ba zasu yi tasiri ba. Kawo yanzu dai an kafa wani kwamitin ƙasa da ƙasa kan wanann batu amma bai riga ya gabatar da rahotonsa ba.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita:            Zainab Mohammed Abubakar