1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar sa ido ta ƙasashen larabawa ta isa ƙasar Siriya

December 27, 2011

A cikin yanayi na zulumi da fargaba tawagar sa ido ta kasashen larabawa ta isa Siriya domin bincike da kuma ganewa idanunta ta'asar da sojojin gwamnati suka tafka.

https://p.dw.com/p/13Zco
epa03016900 (L-R)Arab League Secretary General Nabil Alarabi ,Qatari Foreign Minister Hamad bin Jasim ,Turkey's Foreign Minister Ahmet Davutoglu , Egyptian Foreign Minister Mohamed Kamel Amr attend the Arab Foreign Ministers emergency meeting about Syria,in Cairo, Egypt, 27 November 2011. Arab League Foreign Ministers meet in Cairo later on 27 November to decide whether to rubber-stamp a set of sanctions on Syria drafted by their Economy Ministers after Damascus ignored a deadline designed to end its violent crackdown on protesters. Qatari Foreign Minister Hamad bin Jassim, who heads the league's ministerial committee on Syria, arrived in Cairo early Sunday. Turkish Foreign Minister Ahmet Davutoglu was also expected to take part in the talks. On 26 November, its Economy Ministers drafted a set of sanctions, which include a ban on travel by senior Syrian officials and the suspension of trade links. EPA/KHALED ELFIQI +++(c) dpa - Bildfunk+++
Taron Ministocin ƙungiyar haɗin kan larabawaHoto: picture-alliance/dpa

Tawagar sa ido ta ƙasashen larabawa na shirin fara duba yarjejeniyar da aka cimma da nufin kawo ƙarshen watanni na tarzomar Siriya da ya yi sanadiyar mutuwar dubban jama'a. Masu rajin kare haƙƙin bil Adama na Faransa da kuma Siriya sun buƙaci tawagar ta mutane hamsin wadda kuma ta sauka Siriyar 'yan sa'oi da suka wuce ta zarce kai tsaye zuwa garin Homs inda mazauna yankin suka ce an kashe mutane 20 a jiya Litinin. Ita ma ƙungiyar nazari da kare haƙƙin bil Adama ta Syrian wadda ke da mazauninta a birnin London ta ce sojojin gwamnatin Siriya sun yiwa garin Baba Amr ƙawanya. Tashin hankula sun ƙaru bayan da mutane 44 suka rasa rayukansu a wasu hare haren bama bamai biyu da aka kai wasu gine ginen gwamnati a birnin Damascus a ranar juma'ar da ta gabata. A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya aƙalla mutane 5,000 ne aka kashe tun bayan da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad ta fara dirar mikiya akan masu zanga zangar da ita watanni tara da suka wuce.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi