1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar masu sa ido ta ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta fara ziyara Siriya

December 27, 2011

A wani yunƙuri na kawo ƙarshen rikicin Siriya tawagar sa ido ta ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta fara rangadi a ƙasar, musamman a birnin Homs.

https://p.dw.com/p/13Zk0
In this image from TV shown on the internet made available by the Sham News Network Tuesday Dec. 20, 2011, protesters chant slogans in Homs, Syria. Amateur video emerged on Monday, Dec.19, 2011, from Syria, which purported to show ongoing violence in the restive country. (Foto: Sham News Network, via APTN/AP/dapd) TV OUT THE ASSOCIATED PRESS HAS NO WAY OF INDEPENDENTLY VERIFYING THE CONTENT, LOCATION OR DATE OF THIS VIDEO IMAGE.
Zanga-zanga a HomsHoto: Sham News Network/dapd

Shugabannin 'yan adawar Siriya sun yi kira ga tawagar 'yan sa ido ta ƙungiyar Larabawa da tayi gaggawar zuwa Homs, don ganewa idonta abin da suka kira kisan kare dangi da jami'an tsaron gwamnati keyiwa masu fafutukar sauyi . Sun ce ranar Litinin ma, jami'an tsaron gwamnatin sun hallaka mutane hamsin da bakwai,ishirin da daya daga cikinsu,duk daga jahar ta Hamus. Wani da makami gurneti ya fada kan gidansu ya bayyana halin da garin na Hamus ke ciki;

"Ku kalli irin muggan makaman da suke harbin mu da su,mahaifina yayi shahada,hakama wasu daga cikin makwabtana ,suma sun yi shahada.Ina kuke ne mutanan duniya?Ina kuke yan uwammu larabawa?

Wannan aika-aika da ake zargin jami'an tsaron da tafkawa ya sanya Bassam Ja'ara,daya daga cikin jagororin masu fafutuka a kasar,shima yai kira ga tawagar yan sa idon ta larabawa,kamar haka:

"Ya zama wajibi ga wannan tawaga ta garzaya zuwa garin Hamus,ta shaida wa idonta irin ayyukan ta'asar da jami'an tsaro keyi ,idan ko baza suyi hakan ba,to garama su tattara komatsansu su bar kasar,in ya so,ministocin kasashen larabawa su nemi kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya bawa 'yan kasar ta Siriya kariya"

Ita kuwa kungiyar ta larabawa,ta bakin kakakinta,Ahmad bin Hulli,cewa yayi,ta shirya da mahukuntan na Siriya,kan a wannan Talata,mutane hamsin daga cikin tawagar zasu isa garin na Hamus;

"Tawagar tamu itace take zabawa kanta inda ta ke son zuwa a illahirin cikin kasar ta Siriya,sai dai tana sanar da mahukunta don su baiwa 'yan tawagar tsaro ,ba ma aiki da jitajita,muna da hanyoyinmu na samun rahotanni da kuma tacesu.

Su kuwa mahukuntan na Siriya,cewa su kayi suna maraba da tawagar,don ta ganewa idonta hare hare da 'yan ta'addar ke kaiwa jami'ai da ma'aikatin gwamnati,gami da fararen hular da ba su san hawa ko sauka ba.

"Abin dake faruwa a Humus da Idlib ayyuka ne na kungiyoyin 'yan ta'adda,yadda suke kamewa da kashe bayin Allah,don haka muna fata tawagar zata taimaka wajen kawo karshen wannan zubar da jini,ta kuma fayyace,ko wa yake aikata wadannan ayyukan tarzomar dake da hatsari.

A ta fagen diplomasiyya,kasar Rasha da ta hau kujerar naki,a Majalisar Dinkin Duniya wajen tofin alatsine ga kasar ta Siriya,tace ta yi maraba da zuwan tawagar ta larabawa zuwa kasar ta Siriya,sai dai tayi kashedin cewa,ta samu bayanan asiri dake nuna yiwuwar kai hare hare kan tawagar,da niyar hanata gudanar da aikin ta,don asamu hanzarin da za,a fake dashi wajen kai batin kasar gaban kwamatin tsaro na Majalisar DInkin Duniya,lamarin da zai iya kaiwa ga kutsen kasa da kasa cikin kasar ta siriya.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal