Tawagar Kungiyar Kasashen Larabawa na ci gaba da ziyara a Siriya
December 28, 2011Duk da kasancewar tawagar sa ido ta kasashen Larabawa a kasar Siriya, har yanzu ana ci gaba da aranga tsakanin masu zanga-zanga da dakarun gwamnati.
Saidai a yau hukumomin Siriya sun yi belin mutane kusan 800 daga kurkuku.
Belin firisinoni da janye tankokin yaki daga cikin garurawan da sojoji suka mamaye na daga bukatocin da kungiyar kasashen larabawa ta gabatarwa shugaba Bashar Al-Asad.
A cewar Komitin Koli mai adawa da gwamnatin Siriya, sallamar mutanen 800 na matsasyin wani salo na yaudara da gwamnatin ta bullo da shi, domin karkata hankalin tawagar dake ke ziyara a Siriya.
A wani labarin kuma,ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, ya kiri jikadan kasar Siriya a birnin Berlin domin ya amsa tambayoyi game da harin da wasu mutane su ka kai wa Ferhad Ahma,wani dan adawar kasar Siriya a birnin Berlin.
A wani abu mai kama da jan kunne,Westerewelle ya sanar da jikadan na Siriya cewar, Jamus ba zata amincewa ba, a taka hakin duk wani mahaluki dake cikin kasar.
A daren Litinin ne zuwa safiyar Talata, wasu mutane biyu da ba a tantance ba, suka kai hari gidan Ferhad Ahma, dake birnin Berlin, inda har suka ji masa raunuka.
Ferhad Ahma memba ne a komitin koli da 'yan adawar Siriya suka girka, domin jagorantar gwagwarmayar neman sauyi.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Ahmad Tijani Lawal