1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar AU ta gana da shugaba Ƙhaddafi na Libiya

April 10, 2011

A wani yunƙuri na warware rikicin Libiya Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta aika tawagar da za ta gana da ɓangarorin biyu

https://p.dw.com/p/10r3J
Hoto: AP

Tawagar da Ƙungiyar Tarayyar Ƙasashen Afirka ta AU, ta aika Libiya domin shiga tsakanin rikicin ƙasar, ta isa babban birnin ƙasar wato Tripoli. Tawagar wadda ta ƙunshi shugabanni biyar waɗanda suka haɗa da shugaba Mohamed Ould Abdel Aziz na Mauritania, Amadou Toumani Toure na Mali, da Denis Sassou Nguesso na Congo da ministan harkokin wajen Uganda Henry Oryem Okello, wanda ya wakilci shugaba Yoweri Museveni , ta ƙaddamar da tattaunawar sulhu da gwamnatin shugaba Mu'ammar Gaddafi, a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, inda ta gana da shugaban, kafin ta je ga tattauna da 'yan tawayen da ke Benghazi. A yau lahadi ne dai Ƙungiyar ta AU ta fitar da wata sanarwa, inda ta yi kira ga ɓangarorin biyu su kawo ƙarshen taƙaddamar da ke tsakanin su, amma duk da haka, faɗan ya cigaba da ta'azara a yawancin yankunan ƙasar.

Wani hari da ƙungiyar ƙawance ta NATO ta kai ta sama, ya taimaka wajen jinkirta wani mummunan harin da dakarun da ke goyon bayan Gaddafi suka kai a garin Ajdabiya. Ƙungiyar ta ce ta tarwatsa tankokin yaƙi guda 11 da ke kewaye da garin na Adjadabiya da wasu 14 kuma a wajen garin Misrata da ke ƙarƙashin jagorancin 'yan tawayen ƙasar.

Mawallafiya:Pinaɗo Abdu

Edita: Yahouza Sadissou Madobi