1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar Rasha da Japan

February 11, 2011

Ƙasashen Rasha da Japan za su shiga tattaunawa akan wasu tsibirai da suke taƙaddama akansu tun bayan yaƙin duniya na biyu.

https://p.dw.com/p/10FsP
Masu zanga-zanga a lokacin da Dmitry Medvedev ya kai ziyara a wani tsibiri da ake taƙaddama akaiHoto: AP

A ranar 11 ga watan Fabrairu ƙasashen Rasha da Japan za su shiga tattaunawa domin kawo ƙarshen yaƙin cacar baki da suke yi akan wasu jerin tsibirai. Ganawar da za a yi tasakanin ministan harkokin wajen Japan da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov a birnin Moscow ta zo ne bayan da suka shafe shekaru suna taƙaddama akan tsibiran Kuril da Japan ta bayyanar a matsayin mallakarta da Tarayyar Soviet ta mamaye a ƙarshen yaƙin duniya na biyu. Lavrov ya gargaɗi Japan da cewa ba za a amince da take-takenta ba . Wannan taƙaddamar da ƙasashen ke yi a tsakaninsu ita ce ta hana su sanya hannu akan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin duniya na biyu a hukumance. Shugaban Rasha, Dmitry Medvedev ya ba da shawarar keɓe tsibirin a matsayin yankin walwalar kasuwanci domin jan hankali masu saka jari daga Japan akan kyawawan sharuɗa. A ɗayan hannun kuma buƙatar Japan ita ce samun kafar samar da iskar gas daga wannan yanki.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu