1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An koma tattauna shirin nukiliyar Iran

Ramatu Garba Baba
February 27, 2022

Iran tayi gargadi kan shata mata wa'adi a gabanin ci gaba da zaman tattaunawar shirin nukiliyar kasar da aka soma a wannan Lahadi a birnin Vienna na kasar Austria.

https://p.dw.com/p/47gbk
Österreich | Atomgespräche mit dem Iran
Hoto: EU Delegation in Vienna/Handout/AFP

Gwamnatin Tehran ta ce, ba za ta amince da duk wani wa'adi da kasashen yamma za su shata mata a game da yarjejeniyar nukiliyar 2015 da suka cimma da manyan kasashen duniya ba. Iran ta ce, ya kamata a ci gaba da tattauna yadda za a cimma matsaya guda a maimakon siyasantar da batun a kwan gaba-kwan baya da ake yi.

Wannan na a matsayin martani ga bukatar da kasashen da ke cikin yarjejeniyar suka yi, inda suka nemi karin bayani kan wani shirin makamashin uranium da Hukumar Kula da Makamshin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ta gano a Iran.

A zaman taron da aka soma a wannan Lahadin a birnin Vienna na kasar Austria, kasashen na son ganin Iran ta takaita shirin nukiliyarta domin dakatar da ita daga kera makaman kare dangi da aka ce nada hadarin gaske, a yayin da su kuma za su dage takunkumai na karya tattalin arziki da suka aza wa kasar. Kasashen Britaniya da Chaina da Faransa da Jamus da kuma Rasha da Amirka ne ke kokarin cimma yarjejeniyar.