1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tattalin arzikin Afirka ta Kudu na jan kafa wajen bunkasa

Suleiman Babayo ZUD
March 5, 2024

Hukumar kula da kididdiga ta kasar Afirka ta Kudu ta nuna tattalin arzikin kasar na jan kafa wajen bunkasa abin da zai haifar da sakamako game bangare siyasa na kasar.

https://p.dw.com/p/4dCGK
Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar Afirka ta Kudu
Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar Afirka ta KuduHoto: Rodger Bosch/AFP/Getty Images

Wasu alkaluma da hukumar kula da kididdiga ta kasar Afirka ta Kudu ta fityra a wannan Talata sun nuna yadda ake samun jan kafa wajen samun bunkasa tattalin arziki a kasar, inda bunkasa tattalin arziki na kashi 0.1 cikin 100 aka samu a zango na hudu kuma na karshe a shekarar da ta gabata ta 2023.

Haka ya nuna cewa kasar mafi ingantalin tattalin arziki na zamani tsakanin kasashen Afirka tana cikin tsaka mai wuya na tatalin arziki. Wannan yayin da ake shirin zaben kasa baki daya a wtaan Mayu mai zuwa na wannan shekara ta 2024.

Masu nazabi kan harkokin kasar ta Afirka ta Kudu suna ganin jam'iyyar ANC mai mulki tun kimanin shekaru 30 da suka gabata tana iya rasa rinjayen da take da shi a majalisar dokokin kasar a karon farko, saboda yadda ake ci gaba da samun matsalolin tattalin ariki a kasar.