1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jimami kan kisan Qasem Soleimani

Mahmud Yaya Azare RGB
January 6, 2020

Kisan babban kwamadan dakarun juyin juya halin Iran, Qasem Soleimani na ci gaba da jan hankulan masu fashin baki a game da tasirinsa a siyasar kasar da ma yankin Gabas Ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/3VnGk
Janar Qasem Soleimani
Janar Qasem SoleimaniHoto: picture-alliance/AA/Iranian Leader Press Office

Dan shekaru 62 kafin ya mutu, Janar Qasem Soleimani da ke zama babban kwamandan dakarun juyin juya halin musulunci na Iran, ya shiga kungiya ta baradan juyin juya hali ne, tun a shekarar alifa da dari tara da saba'in da biyu, karkashin jagorancin Ayotullah Khomeni. Irin bajintar da yai ta nunawa a rundunar, musamman a yakin da aka kwashi shekaru goma ana gwabzawa da gwamnatin Iraqi karkashin jagorancin Saddam Hussein, ya ba shi damar samun karin girma, har ta kai shi ga zama jagoran dakarun kundunbala da ake kira “Baradan Qudus” a shekarar alif da dari tara da casa'in. Rundunar da ke ikirarin zama cikin shiri don kwato birnin Qudus mai alfarma daga mamayar Isra'ila.

Iran Trauerzeremonie für getöteten General Soleimani in Teheran |
Dandazon jama'a a yayin jana'izar Janar Soleimani da rundunar sojin Amurka ta halakaHoto: AFP/Office of Iran's Supreme Leader Ayatollah Ali Khamenei


Nasarar da yayi wajen kafa kungiyoyin fafutuka mabanbanta a Iraki, wadanda su kai ta gwagwarmaya da hada baki da ake zargin yayi tayi wajen musayan bayanan sirri da kasashen ketare, musammama kasar Amurka wacce ta kasheshi daga karshe, ya kai ga mamaye kasar Iraqi da tunbuke gwamnatin Saddam ta hanyar rataya.


Nasarar da yayi wajen kirgawa da yin damara ga kungiyoyin 'yan Shi'a a kasashen ketare, kamar irin su Hezbollah a Labanan, wacce a shekarar 2003 ta gwabza yaki da Isra'ila aka tsagaita wuta bayan anyi kare jini biri jini, da kuma Kungiyar Ansarullah ta 'yan Houthi a kasar Yemen, wacce ta mamaye Yemen ta kuma damawa Saudiya da kawayenta lissafi, dama kungiyar Hashdul Sha'abi a Iraqi da Siriya, wacce tai nasarar karya lagon kungiyar IS, tare da hadin guiwa da Amurka wacce ya saba kira da babbar shedaniyar duniya, duk sun sanya masharhanta da jaridun kasa da kasa na kiransa “Kaura ja yaki na kasar” wanda yayi nasarar da tarun ofisoshin jakadanci da jami'an leken asiri suka gaza cimma.

Großbritannien London | Protest gegen US-Krieg mit dem Iran
'Yan Britaniya sun hada gangami don adawa da barkewar yaki a sakamakon kisan SoleimaniHoto: picture-alliance/Anadolu Agency/I. Tayfun Salci


Kasheshi da Amurka tayi dai, inji masharhanata, zai bar gagarimin gibi a kasar Iran da zai yi wuya a cikeshi kwana kusa, a yayin da kasashen da ke zargin yana musu katsalandan a yankin ke zuba ruwa a kasa suna sha, don murnar uwargijiyarsu Amurka ta raba su da alakakai.