1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin China a Afirka

June 3, 2011

Ƙasar China na ci gaba da fafutukar zuba jari da ƙarfafa ma'amallar tattalin arziƙi da nahiyar Afirka, musamman ma a shekarun baya-bayan nan

https://p.dw.com/p/11TnZ
Ma'amallar bankuna tsakanin China da AfirkaHoto: picture-alliance/ dpa

Akwai banbancin ra'ayi tsakanin masana dangane da hada-hadar zuba jari da China take yi a ƙasashen Afirka. A yayinda ƙasashen yammaci ke zargin Chinar da ba da ƙwarin guiwa ga cin hanci, a nasu ɓangaren jami'an siyasar Afirka na zargin ƙasashen na yammaci ne da magana da baki biyu-biyu. Kazalika akwai wasu ƙwararrun dake ganin cewar akan wuce gona da iri a game da batun tasirin China a Afirka. A babban taron mujami'ar Evanjelikan ta Jamus a Dresden sai da aka gudanar da zazzafar mahawara aqkan wannan batu.

Deborah Bräutigam, ƙwararrar masaniya akan al'amuran tattalin arziƙi daga ƙasar Amirka tayi shekara da shekaru tana bin diddigin hada-hadar China a nahiyar Afirka. Bisa ga ra'ayinta dai mayar da hankali da kafofin yaɗa labaran ƙasashen yammaci suka yi akan tasirin China a Afirka, abu ne dake da nasaba da fargabar da ƙasashen ke yi na fiskantar wata sabuwar abokiyar gwagwarmaya a al'amuran tattalin arziƙi da siyasar wannan nahiya. Amma duk wanda yayi bitar alƙaluman dake akwai da idanun basira zai ga cewar China ɗaya ce daga cikin abokan burmin ciniki ga nahiyar Afirka, amma ba ita ce akan gaba ba:

China Afrika Wirtschaft
Tattaunawa tsakanin mata 'yan kasuwa daga China da Najeriya a birnin LagosHoto: AP

"Akwai almara iri-iri a game da rawar China a Afirka. Misali dai cewar China ce sabuwar abokiyar hulɗar ƙasashen Afirka. Amma fa tun a farkon shekaru 1990 ne China ke gabatar da shirye-shiryenta a can. Tun abin da ya kama daga tsakiyar shekarun 1990 kusan dukkan gaggan jami'an siyasar China sun kai ziyara ga illahirin ƙasashen nahiyar. Ɗaya almarar kuma ita ce cewar China na ba da gagarumin taimako ga Afirka. Amma hakan ko kaɗan ba gaskiya ba ce. Yawan taimakon nata bai taka kara ya karya ba. A shekara ta 2008 ma dai yawan taimakon da ta bayar bai kai abin da Jamus ta taimaka da shi ba."

Ko shakka babu game da cewar ba za a iya yin watsi da hada-hadar Chinar a nahiyar Afirka ba, musamman ma idan muka ba da la'akari da cewar a Libiya kaɗai Chinar da kwashe ma'aikata da injiniyoyinta kimanin dubu talatin daga ƙasar sakamakon rikicin da ya rutsa da ita. Amma fa a haƙiƙa China ba ita ce kaɗai abokiyar burmin cinikin ƙasashen Afirka ba, in ji Andrew Mwenda, ɗan jarida daga ƙasar Uganda:

Afrika-China Afrikanische Studenten Handelsbeziehungen Afrika China
Ɗaliban Afirka a ChinaHoto: picture-alliance/ dpa

"China tana cike giɓin ƙoƙarin da ake yi ne na raya makomar Afirka, domin kuwa su ma ƙasashen Turai da Amirka suna ma'amalla da Afirka. Banbancin dake akwai shi ne China tana ba da la'akari da salon rayuwarmu, a yayinda su kuma Turawa suka fi mayar da hankali akan abubuwan da zasu iya canzawa a salon rayuwarmu. Akwai shirye-shiryen ƙasashen yammaci masu tarin yawa a Afirka dangane da yadda za a tsara iyali da amfani da kwararon roba da ma yadda ya kamata a gina gidaje. Wannan abu ne dake ci mana tuwo a ƙwarya, saboda tsarin Afirka ya banbanta."

Sai dai kuma dukkan waɗannan batutuwan ba su da muhimmanci ga Afirka. Ya-alla China ce ko Amirka ko kuma ƙasashen yammaci ke neman yin tasiri a Afirka. Babban abin da nahiyar ke buƙata shi ne a ɗaga matsayinta domin tayi kafaɗa-da-kafaɗa da sauran sassa na duniya da kuma kyautata makomar jin daɗin rayuwar al'umar nahiyar, in ji Cheikh Tidiani Gadio, tsofon ministan harkokin wajen ƙasar Senegal.

Mallwallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal