Tashin hankalin Siriya na ƙara yin muni
July 9, 2012Manzon musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya, Kofi Ananan ya isa a birnin Damaskas inda zai gana da shugaba Bashar al-Assad domin samun mafita ga tashin hankalin da a ka ƙwashe kusan watanni 16 ana faman yi.Mista Annan wanda wannan ita ce ziyara ta ukku da ya ke kaiwa a ƙasar ta Siriya ba tare da samun nasara ba akan yunƙurinsa na diflomasiya na warware taƙaddamar ya na tare ne da rakiyar ƙungiyar ƙasashen Larabawa.
A cikin wata hira da tashar telbijan ta DW shugaba Bashar al-Assad ya soki Amirka da ƙasashen yammancin duniya da ƙara rura wutar rikicin, sannan ya ce kasarsa a shirye take ta tattuana. Ya ce: " kofofinmu buɗe suke ga duk wata ƙasa da ke neman taimaka wa a samu sulhu. Rahotanni daga Siriyar na cewar mutane aƙalla 99 suka mutu a ƙarshen mako a garruruwa daban-daban a cikin yamutsin.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas