1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin hankali a Siriya na ƙara rincaɓewa

July 17, 2012

A yayinda rikicin Siriya ke ƙara tsananta dakarun gwamnati sun fara anfani da jiragen yaƙi akan 'yan tawaye.

https://p.dw.com/p/15Z5V
A Syrian opposition flag is seen at al-Tadamun area in Damascus July 15, 2012. Picture taken July 15, 2012. REUTERS/Shaam News Network/Handout (SYRIA - Tags: CIVIL UNREST POLITICS CONFLICT) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: Reuters

Dakarun gwamnatin Siriya suna yin anfani da jiragen yaƙi masu saukar ungulu wajen ƙaddamar da hare-hare akan 'yan tawaye a dai dai lokacin da faɗa ke ƙara zafafa a Damascus babban birnin ƙasar. Taho mu gama a tsakanin sassan biyu a wasu yankuna huɗu na birnin dai su ne mafi muni a cikin kwanaki ukkun da suka gabata yayin da rikicin na Siriya ke ƙara kusanta da cibiyar mulkin shugaba Bashar al-Assad. Tuni dama dakarun na gwamnati suka fara yin anfani da tankokin yaƙi a faɗan, amma yin anfani da jiragen yaƙi masu saukar ungulu manuniya ce ga rincaɓewar rikicin.

A halin da ake ciki kuma jami'an ƙasar Turkiyya sun sanar da gina sabon sansanin 'yan gudun hijirar dake gujewa rikicin Siriya, wanda zai iya ɗaukar mutane dubu 10 a dai dai lokacin da ɗaruruwan 'yan ƙasar ta Siriya ke tserewa rikicin dake ƙara muni a ƙasar.

Kanfanin dillancin labarai mallakar hukumomin Turkiyya ya sanar da cewar kimanin 'yan gudun hijira 864 ne suka tsallaka ta kan iyakar Turkiyya daga wannan Litinin kaɗai cikin su kuwa harda wani mai riƙe da muƙamin janar da kuma Kanal 4 a rundunar sojin Siriyar.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yawan 'yan gudun hijirar Siriyar da suka nemi taimako a ƙasashen Iraƙi da Jordan da Lebanon da kuma Turkiyya ya riɓanya har sau ukku tun cikin watan Afrilu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar