1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙungiyar tsaro ta NATO a Jamus akan Libiya

April 14, 2011

Ministocin harkokin waje na ƙasashen ƙungiyar na tattauna batun ɗaukar wasu ƙarin matakai akan ƙasar

https://p.dw.com/p/10tGA
Hoto: AP

Ministocin harkokin waje na ƙasashen ƙungiyar tsaro ta NATO na gudanar da wani taro a birnin Berlin na nan ƙasar Jamus.Taron wanda zai maida hankali akan samar da hanyoyin ƙara matsa ƙaimi ga kanal Gaddafin domin tilasta masa barin mulki, ya zo ne a daidai lokacin da aka kammala wani taron a birnin Doha na ƙasar Qatar wanda aka samu saɓani tsakanin ƙasahen da suka amince a taimakawa Libiyar amma ba da makamai ba.

Sakataran Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya na mai cewa ya kammata ƙasashen Duniya su yi magana da murya ɗaya domin ceton al'ummar Libiya.

Tun da farko dai a jajibirin taron na yau na Berlin na ƙwanaki biyu shugaba Nikolas Sarkozy da kuma fraministan Britaniya David Cameron sun jaddada aniyar su ta ƙara ɗaukar matakan kai hare hare akan Libiyar. 

An tsara kuma  ƙungiyar ƙasashen Larabawa za ta gudanar da wani taro ita ma a birnin Alƙahira na ƙasar Masar domin sake tattauna batun.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita  :     Zainab Mohammed Abubakar