Taron ƙasashen larabawa akan Siriya a Iraƙi
March 29, 2012Harin ya zo ne a daidai lokacin da ake bude taron shugabannin ƙasashen larabawa a fadar gwamnatin Irakin a wannan alhamis ɗin. Tuni dai hukumomin Irakin suka sanar da ɗaukar tsauraran matakan tsaro da suka hadar da tura jami'an tsaro dubu 100, zuwa sassa daban daban na birnin na Bagadaza. Daura da wannan an ɗauki matakan takaita zirga zirgan ababan hawa, da ma amfani da wayoyin tafi da gidanka na Salula. Ana saran shugabannin larabawan za su amince da daftarin da jakadan Majalisar Ɗunkin Duniya Kofi Annan ya gabatar dangane da warware rikicin siriya, tare da sanya shugaba Bashar al-Assad ya aiwatar da alkawarin daya ɗauka na amincewa da dukkan batutuwa da aka gabatar. Tuni dai mahukuntan na Siriya suka ce ba zasu bada kai bore ya hau ba, dangane da duk wani batu da za'a ƙirkiro a wannan taro na kasashen larabawan.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal