1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashen duniya akan Siriya

Zainab MohammedJuly 6, 2012

Amurka ta shirya gabatar wa Majalisar Ɗinkin Duniya bukatun ƙaƙaba wa gwamnatin Bashar al-Assad na Siriya saban takunkumi mai tsanani.

https://p.dw.com/p/15SBG
World diplomats attend a "Friends of Syria" meeting at the Dolmabahce Palace in Istanbul June 6, 2012. Seated at the table are (L-R): French Foreign Minister Laurent Fabius, Prime Minister and Foreign Affairs Minister Hamad Bin Jassim Bin Jabor Al-Thani of Qatar, Foreign Affairs Minister Ahmet Davutoglu of Turkey, U.S. Secretary of State Hillary Clinton, Foreign Affairs Minister Saud El-Faisal of Saudi Arabia, Britain's Foreign Secretary William Hague and Foreign Affairs Minister Abdullah Bin Zayed Al Nahyan of the United Arab Emirates. REUTERS/Saul Loeb/Pool (TURKEY - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Wannan kira na Amurka na zuwa ne a daidai lokacin da wakilan ƙasashen sama da 100 na Turai da larabawa dake kiransu kansu "abokan Siriya, ke gudanar da wani taro a birnin Paris. Duk da rahotannin dake nuni da cewar wajen mutane dubu 16,500 ne rayukansu ya salwanta a rigingimun watanni 16 na Siriyan, abokananta Rasha da China basa halartan taron na birnin Paris, duk kuwa da alamun sauyin alkiblar Moscow akan rikicin. Taron na yau dai na zuwa ne bayan waɗanda aka gudanar a biranen Tunis da Istambul, inda kira dangane da ɗaukar matakai masu tsauri kan gwamnatin Bashar al-assad ya ci tura. China dai bata halarci dukkan tarurrukan na baya ba, wanda ya samu halartar ƙasashen Amurka, Britaniya, Faransa, Jamus da kasashen larabawa akarkashin jagorancin saudi Arabiya da Qatar. Akan hanyarta zuwa birnin na Paris, sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta ce lokaci yayi da za'ayi haɗin kai a gaban komitin sulhu, domin ɗaukar matakin matsin lamba akan shugaba Assad.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Yahouza Sadissou Madobi