1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasa da ƙasa kan Afghanistan a birnin Bonn

December 5, 2011

A wannan Litinin ce birinin Bonn ke karɓar baƙi a taron da ake farawa dangane da makomar Afghanistan bayan dakarun ƙasa da ƙasa sun janye, to sai dai maƙociyar ta Pakistan ta ce ba za ta halarci taron ba.

https://p.dw.com/p/13Mbw
Babban sakataren MƊD Ban Ki-Moon da shugaba Hamid Karzai na AfghanistanHoto: AP

Kafin ƙaddamar da taron ƙasa da ƙasa kan Afghanistan a hukumance, da safiyar wannan Litinin a nan birnin Bonn, babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon ya alƙawartawa fadar gwamnatin ƙasar da ke binin Kabul goyon bayansa na wani tsawon lokaci. Bayan wata ganawa da yayi da ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, Mr. Ban ya ce kamata yayi a mayar da hankali a kan abubuwan da ba su shafi aikin soji ba, kuma ya ƙara da cewa dangantakarta da maƙotarta ma yana da mahimmancin wajen kawo daidaito a ƙasar da ta yi fama da yaƙi.

Pakistan na ɗaya daga cikin mahimman ƙasashen da za su iya taimaka wa Afghanistan wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma tabbatar da daidaito a ƙasarta.

To sai dai Pakistan ta janye daga taron sakamakon wani hari da ƙungiyar tsaro ta NATO ta kai kan wasu sansanonin sojin ta biyu da ke kan iyakarta da Afghanistan.

Wannan taron wanda da ake buɗewa a wannan Litinin zai sami halartar ƙasashe 85 da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa guda 16. Wajibi ne mahalarta taron su gabatar da saƙonnin da ke nuna mahimmancin sulhu, domin a cewar Mr. Ban, daidaituwar siyasar Afghanistan bayan dakarun ƙasa da ƙasa sun janye zai yiwu ne kaɗai idan har ta sami goyon bayan maƙotanta.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal