1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sulhun yankin Darfur a Sudan

May 5, 2006
https://p.dw.com/p/BuzW

Taron sulhun shawo kan rikicin yankin Darfur na kasar Sudan da ake ci gaba da gudanarwa a birnin Abujan Nigeria ya tashi baran baran, ba tare da cimma wata matsaya guda ba.

Hakan kuwa ya samo asali ne, bayan da kungiyoyin yan tawaye biyu daga cikin uku suka ki amincewa da daftarin zaman lafiyar da kungiyyar Au ta gabatar.

Masu shiga tsakani daga kungiyyar hadin kann kasashen African wato Au, sun tabbatar da cewa, kungiyyar yan tawayen SLA da tafi kowace girma a kasar da kuma bangaren gwamnati, tuni suka yarda su rattaba hannu akan daftarin sulhun da aka gabatar.

Da sha biyun daren jiya alhamis ne dai wa´adi na uku da kungiyyar ta Au, ta bawa bangarorin na amincewa da wannan daftari ya kare.

Ya zuwa yanzu bayanai sun nunar da cewa masu shiga tsakanin na nan na ci gaba da kokarin ganin an samo bakin zaren warware wannan rashin fahimtar junan a tsakanin bangarorin da abin ya shafa.