1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TARON RAGE TALAUCI A BURKINA FASO.

September 8, 2004

Yau ne shugabannin Afrika 17 ke taron samarda hanyoyin yaki da rashin aikinyi a tsakanin jamaa.

https://p.dw.com/p/BwVP
Kungiyar gamayyar Afrika,AU.
Kungiyar gamayyar Afrika,AU.Hoto: AP

A yau ne ake bude taron wasu kasashen Afrika a babban birnin kasar burkina faso dake Ouagadougou,domin tattauna shirin samarda da aikinyi wa miliyoyin yan Nahiyar dake fama da talauci,da inganta cigaban wannan yanki.

Shugaba Blaise Compaore,na Burkino Faso wanda yayi jawabin bude taron,ya marabci takwarorinsa da suka fito daga kasashe 16,da nufin tsamo nahiyar Afrika daga kangin talauci datake fama dashi.

A karkashin shugabancin Shugaba Olusegun Obasanjo na Nigeria,kuma shugaban kungiyar gamayyar Afrika,taron zai tattauna hanyoyi da za abi domin kawo karshen rashin aikinyi da rashin ingantacciyar cigaba,wanda ya haifar da tsaiko wajen samarda aikin biya wa kashi 3 daga cikin 4 na yawan jamaar nahiyar.

Bukatar Zuba jari cikin harkokin noma ,wanda ke zama mafi girman bangaren tattalin arzikin nahiyar,da kananan manoma wadanda yawansu yakai million 225 daga cikin adadin mutane million 300 dake cikin kunci na talauci,na daya daga cikin muhimman batutuwa da wannan taro na shugabannin kasashe 17 ,zasu tattauna akai,a taron na yini biyu.

Bugu da kari ana saran tattauna hanyoyin taimakawa miliyoyin mutane matalauta dake zama a birane ,musamman mata,a manyan biranen Afrika da suka hadar da Lagos,Kinshasa da Johanesburg,ta hanyar samar musu aikinyi da wadataccen biya.

Nahiyar Afrikan dai ta dauki mataki na inganta tattalin arziki,inda aka samu cigaba daga kashi 3 da digo 2 daga cikin 100 a shekarata 2002,zuwakashi 4 da digo biyu daga cikin 100 a shekara data gabata,to saidai wannan ba wani abun kuzo ku gani bane wajen samarwa miliyoyin mutane nahiyar aikin yi.

Anyi kiyasin cewa idan ba matakai na gaggawa aka dauka ba,nan da shekarun 2015 ga mai rai,adadin marasa aikinyi zai dada karuwa,a akasarin kasashen afrika.

Shi kuwa shugaban kungiyar kwadago ta kasa da kasa Juan Somavia cewa yayi,inganta tattalin arziki da watsi da samarda aikinyi,bazai kawo wani cigaba ba,dole ne a mayar da hankali wajen samarda da ayyukanyi wa jammaa,kafin a mayar da hankali kann gyare gyare na tattalin arziki.

Ayanzu haka dai kididdiga na nuni dacewa akwai kimanin mutane million 320,a kasashe 34 dake yankin kudu da sahara,dake rayuwa cikin kunci na talauci,inda suke rayuwa akan kudi kasa da dala guda a kowane yini daya.An kuma bayyana yankin da kasancewa wuri da rayuwa ke dada tabarbarewa acikin shekaru 20 da suka gabata,inji hukumar inganta rayuwa ta mdd,ayayinda ita kadai ce bazata cimma burin da majalisar ta sanya gaba,na cigaba nan da shekarata 2015 ba.

Zainab Mohammed.