1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron NATO game da yaƙin Libiya

March 25, 2011

Ƙungiyar Nato za ta fara jagorancin aikin hana zirga zirga jiragen sama a sararin samaniya ƙasar Libiya

https://p.dw.com/p/10hCa
Anders Fogh Rasmussen Sakataren ƙungiyar tsaro ta NATOHoto: AP

Wakilan ƙasashe guda 28 membobin ƙungiyar tsaro ta NATO sun amince da karɓar ragamar jagorancin aiki hanna jiragen sama ƙasar Libiya shawagi a sararin samaniyar ƙasar. ƙasashen sun cimma wannan shirin ne a taron da su ka yi a birnin Brussels na ƙasar Beljiam wanda ya tanadi yin amfanin da ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya na aya 1973.

Sakataran Ƙungiyar NATO Anders Fogh Rasmussen ya shaida cewa ƙasashen Faransa da Ingila da´kuma Amurka su za su kula da aikin kare fara fula a ƙasar ta Libiya.ko da shike akwai saɓanin ra'ayoyi tsakanin ƙasashen wajan yadda za a ci gaba da yin aiki amma ministan harkokin waje na Ingilia William Hague ya ce akwai buƙatar ƙara samun haɗin kawuna na ƙasashen.Su na buƙatar ƙaddamar da aikin jagorancin cikin haɗin kai kuma su na fatan hakan zai samu.

Mawallahi: Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi