1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

061011 NATO Verteidigungsminister-Treffen

Zainab MohammedOctober 6, 2011

Ministocin tsaro na asashe membobin NATO sun kammala taron yini biyu da suka gudanar a birnin Bruxelles na Beljium game da fada da ke ci gaba da gudana a Libya da kuma yakin da ayyukan ta'addanci a kasar Afhganistan.

https://p.dw.com/p/12mxC
Sakataren NATO Anders Fogh Rasmussen ya na tattaunawa da wasu ministocin tsaroHoto: picture alliance/dpa

Dama dai bisa ga al'ada wadannan ministocin tsaro na kasashe da ke da kujera a kungiyar tsaro ta NATO ko OTAN ba sa gudanar da taronsu ba tare da sanya batun yaki da suke yi da ayyukan ta'addanci a Afghanistan a agandar su ba. Sai dai taron na bana ya zo ne a daidai lokacin da kasashen suka fara janye dakarunsu daga wannan kasa, shekaru goma cif da kaddamar da sa kafar wando guda da suka yi da masu tsatsauran ra'ayin addinin musulunci na taliban.

Egon Ramms mit Hamid Karzai und Dan McNeill
Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan da wasu hapsoshin sijojin NATOHoto: picture-alliance/ dpa

Hasali ma dai sun tsayar da shekara ta 2014 a matsayin lokacin da kasashen na NATO ko OTAN za su tattara nasu ya nasu su fice daga kasar, tare da sakar wa dakarun Afghanistan wuka da namar tafiyar da harkokinsu na tsaro. Sai dai sakataren tsaron Amirka Leon Panetta ya ce ya zama wajibi a guje janye dakaru cikin gaggwa a Afghanistan idan dai ba a son a bayar a kura.

"Amirka za ta tabbatar cewa lokacin da za ta janye dakarunta ba ta jefa sauran takwarorinta na NATO cikin matsalar ba domin kuwa zai iya yin tasirin akan rayukan sojojinta."

Wannan ya na nufin cewa wasu sojojin kundumbala, da wasu jiragen yaki masu saukar angulu, za su ci gaba da zama a kasar ta Afghanistan. ko suma kasashe Turai da ke da kujera a NATO ko OTAN suna nazarin irin gudunmawar da za su bayar domin a tabbatar da cewa janye dakaru da kuma mika wa sojojin Afghanistan harkokinsu na tsaro ya gudana ba tare da wata matsala ba. A halin yanzu dai kasashe 17 ne suka amsa kirar da ta Jamus ta yi musu a inda suka yi aika da dakarunsu a yankin Arewacin Afghanistan da ke karkashin kulawar Bundeswehr wato majalisar tsaro ta tarayyar Jamus. Ministan tsaro Jamus Thomas de Maiziere ya ce wannan mataki na hada karfi da karfe zai hana su jin kunya bisa manufa.

Verteidigungsminister Thomas de Maiziere
Ministan tsaro Jamus Thomas de Maiziere da 'yan jarida a hanyar ta zuwa AfghanistanHoto: dapd

"Burin da aka sa a gaba shi ne a samar da manufa ta bai daya game da abin da ya shafi ayyukan tsaro a arewacin kasar kama daga danka wa sojojin Afghanistan wannan aiki, har i zuwa janyewa da za mu yi a shekara ta 2012."

Babu dai wata kasa ta NATO da ta fito fili ta bayyana yaushe za ta kwashe gaba dayan dakarunta a Afghanistan. abin da kawai ya fito fili yanzu haka shi ne Amirka za ta janye 10 kafin karshen wannan shekara yayin da za ta janye wasu karin 23 kafin watan satumba na 2012. sauran kasashen da ke da kujera a kungiyar tsaro ta NATO suka ce wannan mataki zai danganta da halin tabarbarewa ko kuma ingatuwar harkokin tsaro a wannan kasa. Sai dai a karon farko adaidin hare-haren ta'addnci ya ragu matika a watannin Juli da kuma Agusta.

Ita ma dai gwamnatin Jamus ba ta bayar da karinhaske game da jadawalinta na janye dakaru ba. sai dai tuni ta wanke hannayenta daga harkokin tsaro na manyan biranen lardunan afghanistan. kana tace sannau akan hankali za ta mayar da harkar tsaron wasu gundumomi karkashin kulawar sojojin na Afghniatan kan nan da farkon watan nowamba. Lamarin da zai yi tasiri kan manufar gwamnatin jamus game da yaki da ayyukan ta'addanci a afghanistan.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar