1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin kuɗi na ƙungiyar G20

October 14, 2011

Shugabanni Turai na samun hadin kai wajen warware matsalar tattali a nahiyar

https://p.dw.com/p/12sM4
Hoto: AP

Bayan ganawarsu a birnin Paris, Ministocin kuɗi na Faransa da Jamus sun sanar da cewar, ƙasashen biyu na aiki tare domin ɓullo da tsarin shawo kan matsalolin basussuka. Ministan kuɗi na tarayyar Jamus Wolfgang Schaeuble da takwaransa na Faransa Francois Baroin, sun gana ne gabannin fara taron yini biyu na ministocin kuɗi na ƙasashen kungiyar G20. Taron ya taimaka wajen tantance wani shiri da shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel suka gabatar. A cewar ministan kuɗin na Faransa, shirin na da nufin daidaita ƙakashen da ke amfani da takardar kuɗi na euro, kalubalantar matsalar Girka, samar da da sauyi a dokokin kuɗaɗen ceto, kazalika da cimma matsayar ƙarin jari wa Bankuna.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal