1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin EU kan Girka da Spain

May 14, 2012

Ministocin Kungiyar Tarayyar Turai(EU) za su hallara a birnin Brussels na kasar Beljiyam don duba hanyoyin samun mafita daga halin da ke wakana a Girka da Spain

https://p.dw.com/p/14uni
EU Commissioner for the Economy Olli Rehn addresses the media on the spring economic forecast at the European Commission headquarters in Brussels, Friday May 11, 2012. (Foto:Geert Vanden Wijngaert/AP/dapd)
Olli Rehn , shugabar hukumar kudin EUHoto: AP

A yau Litinin (14. 05.2012) ne ministocin kuɗin ƙungiyar Tarayyar Turai ke gudanar da taro a birnin Brussels na ƙasar Beljiyam domin duba halin da nke wakana a ƙasashen Girka da Spain. A baya ga haka za su kuma tattauna batutuwa da dama da suka haɗa da ba da ƙarin muƙamai cikinsu har da na shugaban ƙasashen ƙungiyar. A dai ƙarshen watan Yuni mai zuwa ne firaminstan Luxembourg, Jean Claude Junker zai cika wa'adin aikin a matsayinsa na shugaban ƙungiyar ministocin kuɗin ƙasashen Turai da ke amani da takardar kuɗin Euro a ƙungiyar. Ana dai kallon Wolfgang Schaeuble, ministan kuɗin Jamus a matsayin wanda zai maye gurbinsa. To amma ko da yake shi kuma ya bayyanar da niyyarsa ta riƙe wannan muƙami, nada shi a matsayin, ya dogara ne akan amincewar sabon zaɓaɓɓen shugaban Faransa, rancois Hollande wanda har yanzu bai bayyanar da matsayinsa game da hakan ba.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Saleh Umar Saleh